“Na Zata Zan Yi Aure Ina Da Shekaru 22 Sannan Na Haifi Yara 2”: Dirarriyar Budurwa Ta Amarce a 27

“Na Zata Zan Yi Aure Ina Da Shekaru 22 Sannan Na Haifi Yara 2”: Dirarriyar Budurwa Ta Amarce a 27

  • Wata kyakkyawar budurwa wacce ta tsara yin aure a shekaru 22 sannan ta zama uwa kafin 25 bata cimma burinta ba
  • Ta yi aure shekaru biyar bayan lokacin da ta so, inda ta wallafa bidiyo tana mai sanar da mutane cewa abubuwa basa tafiya yadda muke so
  • Yan mata da dama a sashinta na sharhi sun jinjinawa gaskiyarta, yayin da wasu suka ce bidiyon ya karfafa masu gwiwa

Wata matashiyar budurwa a TikTok, @preshie07_21, ta wallafa bidiyon yadda rayuwarta ya sauya ba kamar yadda ta tsara ba. Matashiyar ta ce burinta a kullun shine ta yi aure sannan ta zama uwa tana da shekaru 22.

Da take nuna shagalin bikin aurenta, matar ta ce ta yi aure tana da shekaru 27 kuma har yanzu bata haihu ba. Wani bangare na bidiyon ya nuna yadda aka yi bikin auren.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Gobara Ta Tashi Ana Tsaka Da Shagalin Bikin Aure, Jama'a Sun Ci Na Kare

Matashiyar budurwa da angonta
“Na Zata Zan Yi Aure Ina Da Shekaru 22 Sannan Na Haifi Yara 2”: Dirarriyar Budurwa Ta Amarce a 27 Hoto: @preshie07_21
Asali: TikTok

Yan sakonni cikin bidiyon, sai aka ganota sanye da doguwar riga fara irin ta amare tare da angonta sanye da kwat. Ta yi wa bidiyon take da:

"Wasu lokutan abubuwa basa tafiya yadda aka tsara."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

AdaUgwu Tv ya ce:

"Ke kasai ce kika fadi gaskiya a kan wannan gasar. Ina tayaki murnar aurenki."

Essenceta ce:

"Ke kin ma gani a 27, ki godewa Allah kan naki. Wasunmu sun fara cire kauna a shekaru 30. Allah ya yi mun irin naki."

Stitchesbyomahz ta ce:

"Nima a shekaru 22 na so yin aure amma yanzu shekaruna 28 tare da masoyin raina."

nemelum33 ta ce:

"Ke kadai ce kika fadi gaskiya...Ina tayaki murnar aure yar'uwa."

favourmicheal2333 ta ce:

"Shekaru mafi dacewa da mutum zai yi aure."

Mobola ta ce:

Kara karanta wannan

“Sun Yi Kaman Uwa da ‘Da”: Bidiyon Shirgegiyar Mata Da Sahibinta Dan Tsurut Ya Girgiza Intanet

"Na tayaki murna shekaruna 27 kuma har yanzu bani da tsayayye."

Kingchinny01 ya ce:

"Allah ya yi maki albarka naki ne kawai ya yi mun dadi."

opeyemi oladeji ta ce:

"Nagode sosai na ga wani bidiyo jiya sai na kalli kaina wato shin daidai nake na tsara yin aure a shekaru 21 yanzu shekaruna 27 zanyi aure a shekarar nan."

Matar aure ta karrama uwar mijinta a wajen shiga mota

A wani labarin, wata matar aure ta sha jinjina bayan ta karrama surukarta ta hanyar bata damar zama a gaban mota kusa da danta yayin da za su fita unguwa tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel