CBN Zai Fara Garkame Asusun Bankin da Ba a Hada Shi da BVN Ba a Najeriya

CBN Zai Fara Garkame Asusun Bankin da Ba a Hada Shi da BVN Ba a Najeriya

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) zai garkame dukkan asusun banki a kasar wadanda ba su da lambar BVN don rage yawaitar damfara
  • BVN wasu lambobi ne da ake ba duk wani wanda ya bude asusun banki a Najeriya don tantance gaskiya da sahihancin kwastoma
  • Akwai akalla bankuna 24 na kasuwanci a Najeriya, ciki har da Access, UBA, Zenith da dai sauransu da ke bukatar BVN kafin bude asusu

CBN ya sanar da cewa, zai fara rufe asusun bankin mutanen da basu da lambar tantancewa ta BVN a kasar nan, Ripple Nigeria ta tattaro.

Blaise Ijebor, wani babban darakta a asashen hadarin kudi na CBN ya bayyana cewa, ya zama dole kowa ya bude asusu da BVN a kasar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 6 ga watan Afrilu a yayin wani taron da aka gudanar game da rage yawaitar sace kudaden mutane ta yanar gizo a kasar.

Kara karanta wannan

NSCDC Sun Damke Wasu Masu Buga Nairori da Dalolin Karya a Jihar Zamfara

CBN zai fara rufe asusun bankin da ba BVN
Yadda kudaden Najeriya ke daukar hankali | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Menene BVN?, kuma meye amfaninsa?

BVN dai wasu lambobi guda 11 da ake ba mutumin da ke son bude asusun banki a Najeriya don tabbatar da sahihancin bayanan kwastoma da kuma kiyaye aukuwar ayyukan damfara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake karin haske, Ijebor ya ce, babban bankin na aiki tare da hadakar bankuna na NIBSS don dakile yawaitar damfara a fannin bankuna.

Duk da cewa ya ce CBN zai yi wannan aikin na rufe asusun nan kusa, amma bai bayyana yaushe ne za a aiwatar da hakan ba.

Wadanne irin asusu za a garkame, kuma wadanne ne ake dasu a kasar?

Asusu na farko a Najeriya shine ‘Tier-1’ wanda ke ba kwastomomi damar bude asusun da za su iya ajiye wani adadi na kudin da bai taka kara ya karya ba.

Kara karanta wannan

An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

Akwai kuma ‘Tier 2’ da ke ba kwastoma damar bude asusu cikakke tare da amfani da lambar BVN da ake amfani dashi a kasar.

A yanzu haka, CBN ya ce zai kawo hanyar da za ta taimaka wajen tabbatar da yiwa masu asusun ‘Tier 1’ BVN tare da kaurar dasu zuwa ‘Tier 2’.

Bankuna sun shiga damuwa, jama’a sun daina kai kudadensu banki

A wani labarin, kunji yadda wasu bakuna a Najeriya ke nuna rashin jin dadinsu ga yadda kwastomomi suka rage kawo kudade.

Wannan ya faru ne bayan da aka sha wahalar neman takardun kudade a bankunan kasar nan daban-daban.

An ruwaito cewa, jama’a sun rage kai kudinsu banki ne tare da ajiye kudaden a gida an fadi illar yin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel