NSCDC Sun Damke Wasu Masu Buga Nairori da Dalolin Karya a Jihar Zamfara

NSCDC Sun Damke Wasu Masu Buga Nairori da Dalolin Karya a Jihar Zamfara

  • Hukumar NSCDC ta kama wadanda ke da hannu wajen bugawa da yawo da kudin jabu a Zamfara
  • Asirinsu ya tonu ne da wani a cikinsu ya biya kudin mota da N1000 ta jabu, sai aka bankado shi
  • Idan an karkare duk wasu binciken da za ayi, za a gurfanar da wadannan mutane da ake zargi a kotu

Zamfara - Dakarun hukumar NSCDC na reshen jihar Zamfara sun cafke wasu mutane uku da ake zargi su na da hannu wajen buga kudi na bogi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Kakakin NSCDC na Zamfara, Ikor Oche ya bada sunayen wadanda aka cafke da Kamalu Sani da Suleiman Yusuf.

Na ukun su shi ne Uzaifa Muazu, ana zargin su da laifin buga takardun Naira da Daloli na bogi. Idan an gama bincike, za ayi shari'a da su a kotu.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Dawo Ɗanye, APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Da Wani Babban Jigo

Oche yake cewa mutanen sun shiga hannu ne yayin da wani direban Keke Napep mai suna Umar Nasir ya shigar da kara bayan sun damfare shi.

Yadda asiri ya tonu

Umar Nasir yana zargin cewa daya daga cikin wadanda ake tuhuma ya ba shi N1000 ta karya, sai bayan an biya shi kudin aikinsa ne ya lura da hakan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A ranar 3 ga watan Afrilu 2023, wani Kamalu Sani mai shekara 28 ya dauki hayar Keke Napep daga kasuwa da kusan karfe 1:00 nr.
NSCDC
Keke Napep Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Daga isa inda zai sauka, sai ya ba direban Keke Napep din takardar N1000 wanda aka gano ta bogi ce.
Direban keken, Umar Nasir, ya kai kara wanda ya yi sanadiyyar cafke wanda ake zargi, Kamalu Sani.”

- Ikor Oche

Tashar Channels ta rahoto Oche yana cewa dakarunsu na NSCDC sun iya kama wanda yake raba kudin jabun a garin Kwatarkwashi da ke jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kame tsagerun 'yan bindiga 2 da suka addabi jihohin Arewa

Wani Muazu Abdulkarim ne ake tuhuma a matsayin shugaban masu wannan aika-aika, yana hada-kai da ‘dansa, Uzaifa Muazu wajen damfarar mutane.

Rahoto ya zo Sani ya amsa cewa fiye da shekara kenan yana amfani da N1000 na karya. Zuwa yanzu an karbe N60,000 da fam $2,600 daga hannunsu.

Shari'ar Daniel Bwala da EFCC

An ji labari Barista Daniel Bwala zai yi shari’a da Jam’iyyar APC a babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja saboda bashin da ya ce an ki biyansa.

Lauyan ya ce ya yi wa APC aiki a Kuros Riba, Osun, Kaduna, Benuwai, Ondo da Abuja, ba a biya shi ba, aka toye masa hakkinsa saboda ya bi Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel