Bayan Yi Masa Tonon Silili, Peter Obi Ya Ce an Matsa Masa Lamba Ya Bar Najeriya, Ya Caccaki APC

Bayan Yi Masa Tonon Silili, Peter Obi Ya Ce an Matsa Masa Lamba Ya Bar Najeriya, Ya Caccaki APC

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya yi martani game da batun faifan muryarsa da ke yawo
  • A cewarsa, muryar ta bogi ce, kuma ana ci gaba da matsa lamba kan ya bar Najeriya saboda wasu dalilai
  • A baya, gwamnatin Najeriya ta ce, Peter Obi ya ci amanar kasa, inda daga baya ya yi martani mai zafi ga ministan yada labarai

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya bayyana cewa, yana fuskantar matsin lamba kan ya bar Najeriya.

Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a shafin Twitter, inda ya caccaki jam’iyyar APC da hukumomin gwamnati, kana ya zarge su da yada farfaganda.

Tsohon gwamnan na Anambra ya ci gaba da bayyana cewa, faifan muryarsa da ke yawo a lokacin da yake magana da wani fasto ba gaskiya bane, na bogi ne.

Kara karanta wannan

Easter: Buhari ya ba da hutun kwana 2 a Najeriya, ya roki 'yan Najeriya wata alfarma

Peter Obi ya ce an matsa masa ya abr Najeriya
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a Najeriya na Labour | Hoto: reubenabati.com.ng
Asali: UGC

Idan baku manta ba, an yada wani faifan murya da ke nuna cewa, Peter Obi ya ce zaben shugaban kasa na bana lamari ne da ya shafi yaki tsakanin addinin Islama da Kiristanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin Peter Obi game da batutuwan da ake yadawa

A cewar sanarwar da ya fitar:

“Yunkurin APC a matsayinta na jam’iyya da kuma gwamnatin APC ta hanyar amfani da jami’an gwamnati da hukumomi wajen kawar da hankalinmu ga hakkinmu da aka kwace abin takaici ne.
“Wannan na zuwa kuma na ci gaba da yaduwa ta hanyoyi da yawa, misali ikrarin sharri na ministan yada labarai Mr Lai Mohammed, bazuwar faifan murya da kuma matsin lamba gare ni kan na bar kasar.
“Bari na kara jaddada cewa faifan muryan da ke yawo na bogi ne, kuma ban taba fadi ba a lokacin kamfen ko yanzu cewa, ko na yi tunanin ko ma dai na ayyana cewa babban zaben 2023 yaki ne na addini.”

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fadi Munanan Barazanar da Ake Fuskanta a Yau a Najeriya

Ban ci amanar kasa ba, martanin Peter Obi ga minista Lai Mohammed

A wani labarin, kun ji yadda Peter Obi ya bayyana cewa, bai ci amanar kasa ba, kuma gwamnatin APC ce mai yada karya a Najeriya.

Obi ya fadi hakan ne a martaninsa ga kalaman ministan yada labarai Lai Mohammed game da wani faifan murya da ke yawo na dan takarar.

A cewar majiya, Peter Obi ya ce, zaben shugaban kasa na 2023 ba komai bane face fagen yaki tsakanin addinin Kirista da Islama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel