Bankuna Sun Shiga Tashin Hankali, ’Yan Najeriya Sun Daina Zuba Kudadensu a Banki

Bankuna Sun Shiga Tashin Hankali, ’Yan Najeriya Sun Daina Zuba Kudadensu a Banki

  • Bankunan Najeriya sun fara kokawa kan yadda kwastomomi ke kin kawo kudi bankuna a cikin wannan yanayin
  • Majiyoyi daga wani banki sun ce, wannan lamari ba karamin hadari bane ga tsarin bankuna kuma zai shafi tasirinsu
  • A bangare guda, karancin sabbin N200, N500 da N1000 ya fara zama babban abin damuwa ga ‘yan Najeriya da yawa

Bankuna a Najeriya sun fara kokawa kan yadda ‘yan Najeriya suka daina kawo kudi banki, kamar yadda majiyoyi suka bayyana wa Legit.ng a karshen mako.

A cewar wasu ma’aikatan banki, rashin kawo kudi banki zai kange su daga ba da bashi da sauran hada-hadar kudi don habaka kasuwanci a kasar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, mambobin kwamitin ajiyan kudi a bankuna na DMB sun bayyana cewa, rashin dawo da kudi bankuna barazana ne ga tsarin banki a kasar.

Yadda 'yan Najeriya suka daina kai kudi banki
Rashin kai kudi banki na damun bankuna | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Masu hasashe sun bayyana cewa, barazana ce babba ga bankuna idan ‘yan kasa ba sa dawo da kudi ta hanyoyi daban-daban.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun kuma bayyana cewa, da irin wannan yanayin, Najeriya za ta koma gidan jiya na karancin kudade a hannun jama’a.

Yadda karancin kudi ya daidaita abubuwa a Najeriya

A kwanakin baya, sauyin kudi da sabbin dokokin CBN sun jawo tsaiko ga harkokin ‘yan Najeriya, lamarin da ya sa wasu ke ajiye kudadensu a gida a madadin kai wa banki.

Masana sun ce, ajiye kudi a gida zai shafi bankuna, zai rage damar ba da rance, zuba hannun jari da kuma tafiyar da harkokin yau da kullum.

Rahotanni sun bayyana cewa, a makwanni biyu da suka gabata, CBN ya saki tsoffin kudade sama da Naira tiriliyan 1 a kasar, kudaden da aka tattara ne bayan sanya dokar sauyin kudi.

Gwamnan CBN ya ce an saki kudade

A wata ganawa da aka yi da gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya ce babban bankin ya saki kudade da yawa domin bukatar ‘yan kasa.

Wannan lamarin dai ya zo da batu mai kama da toshe bakin ‘yan kasar game da batan yawaitar yawon sabbin takardun kudin da aka buga.

‘Yan Najeriya da yawa na kukan cewa, karancin sabbin kudin ya fara zama damuwa a cikin mutane, inda wasu ke tambayar ko dai kudaden da CBN din ya kashe biliyoyi wajen bugawa sun kare ne.

Akwai laifin bankuna, inji masani

Muhammad Jibrin, wani masanin tattalin arziki a jami’ar Bauchi ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa cewa:

“Kamar lamarin ya dawo kan bankuna ne. A farko sun yi ta nunawa mutane wulakanci wajen ba da sabbin kudi. Yanzu yardar ‘yan Najeriya ta kare a kansu, kowa na tsoron me zai biyo baya.
“Wannan ne yasa da zarar wasu sun samu kudi gwara su ajiye a hannunsu a madadin kai wa banki, domin idan suka je banki cire kudi sai ransu ya baci, kuma laifin bankunan ne.

“Ba abu ne mai kyau ba, ya kamata a mayar da kudade banki saboda ci gaban tattalin arziki, don haka ‘yan Najeriya su yi hakuri su karbi canjin da aka samu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel