Messi Zai Bar PSG: Manyan Kulob Guda 6 da Ke Zawarcinsa, Da Kuma Hasashen Inda Zai Koma

Messi Zai Bar PSG: Manyan Kulob Guda 6 da Ke Zawarcinsa, Da Kuma Hasashen Inda Zai Koma

  • An rahoto cewa, akwai yiwuwar Lionel Messi ya sake rattaba hannu kan yarjejeniyar buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta PSG
  • Dan wasan mai shekaru 35 na kan ganiyar cike wa’adin yarjejeniyar da ya dauka na buga wasa a PSG har zuwa karshen zango
  • Sashen wasanni na Legit.ng, Sports Brief ya yi bincike, ya hada rahoto game da kulob-kulob din da Messi ka iya komawa idan bai zauna a PSG ba

Ana kyautata zaton cewa, watakila Lionel Messi ya yi sallama da kungiyar kwallon kafan Faransa ta PSG a karshen zangon 2022/2023.

Dan wasan na gaba mai shekaru 35 a yanzu haka yana PSG, kuma zamansa ya kusa karewa kasancewar yajejeniyarsa da kulob din zai zo karshe nan kusa.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, nasarar da Argentina ta samu a watan Disamban bara a wasan kofin duniya ya ba Messi damar yin shawari game da makomarsa a PSG.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Buhari Ta Zargi Peter Obi Da Cin Amanar Kasa

Inda Messi zai iya komawa bayan barin PSG
Lionel Messi, fitaccen dan wasan duniya | Hoto: @barcauniversal
Asali: Twitter

An kuwa naqalto cewa, dan wasan ya samu tayi daga kungiyoyin kwallon kafa na duniya masu yawa, kuma zai duba a tsanake kafin zaban daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da wasu manyan kungiyoyi ke neman Messi, mun tattaro muku manyan kungiyoyi shida da watakila zai shige cikin daya idan ya bar PSG.

Newcastle

Babu kulob din da ba za ta so Messi ba. Don haka Newcastle na daga cikinsu. Kungiyar na da kudi saboda tallafin da take dashi daga Saudiyya.

Zai zama ba komai bane ga kulob din siyan Messi, kasancewar ta sha kudi a baya-bayan nan da kuma lura da irin kashe kudin da take.

Messi dai bai taba buga wasa a wasannin Premier League ba, amma watakila ya samu dama a yanzu idan Newcastle ta dauko shi.

Manchester City

Baya ga Newcastle, Messi zai iya samun damar buga Premier idan ya shiga kungiyar kwallon kafan Turai ta Manchester City.

Kara karanta wannan

Kaman Almara: Wani Dan Najeriya Ya Yi Tafiya Kan Ƙwai Ba Tare Da Sun Fashe Ba, Bidiyon Ya Yaɗu

Messi dai ya buga wasanni masu kyau, ya kuma taka rawar gani a alakarsa da Pep Guardiola. Sake haduwarsu a Manchester City zai ba da citta matuka.

Tarihi ya nuna yadda dan wasan ya samu manyan nasarori a shekarun baya tare da Guardiola a gefensa.

Al Hilal

Al-Hilal ce daya daga cikin manyan kungiyoyin kafa na Saudiyya. Sun yi tayin hada hamayya tsakanin Messi da Ronaldo a kasar ta Larabawa.

A yin hakan, Al-Hilal a shirye take ta ba da kudin da ya kai $300m ga Messi a shekara don fafatawa da Ronaldo a wasannin kasar.

Ba Messi wadannan kudaden zai sanya shi ya zama dan wasan kwallo mafi samun dukiya mai yawa, inda Ronaldo zai zama na biyu da $215m duk shekara.

Zai ba da citta a ce ga Ronaldo a Al-Nassr ga kuma Messi a Al-Hilal; kamar Barca da Real Madrid ne.

Inter Miami

Akwai yiwuwar Messi ya shilla kasar Amurka, domin wata kungiyar kwallon kafa a can ta nemi ya zo bayan cikar wa’adinsa a PSG.

Kara karanta wannan

“Ba Za a Rantsar Da Tinubu Ba:” Magoyin Bayan Peter Obi Ya Fasa Ihu a Bidiyo, Ya Hana Jirgin Sama Tashi

Kungiyar Inter Miami da ke Amurka na kwallafa rai ga zuwan Messi bayan barin PSG don buga wasannin MLS a kasar.

Inter Miami na da kwarin gwiwar zuwan Messi kasancewar tattaunawa tsakanin tsaginsa da na su ya fara nisa na tsawon shekaru.

Masu kungiyar Inter Miami, Jorge da Jose Mas tare da David Beckham na ci gaba da magana kan lamarin, suna ma magana da mahaifin Messi, Jorge Messi.

Newell's Old Boys

Messi ya fara wasansa ne a Newell’s Old Boys ta Argentina a matsayin matashi kafin daga bisani ya koma Barcelona; ya shafe shekaru biyar a can.

An ruwaito cewa, Messi ya ci kwallaye sun kai 100 a lokacin da yake kulob din kafin ya shigo Barcelona, inda ya fi shahara kenan.

A wani lokaci, Messi ya taba bayyana cewa, zai so komawa Newell’s Ondo Boys saboda wasu dalilai da ya bayyana. Ga shi suna nemansa yanzu.

Kara karanta wannan

Ramadana: Hisbah ta fasa kwalaben barasa na N500 a jihar Kano, ta yi wani bayani

Barcelona

Rahotonmu na baya ya bayyana yadda kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ke zawarcin Messi a wannan karon domin sake dawowa gida.

An ruwaito cewa, mataimakin shugaban kungiyar kwallon kafan ya fara tattaunawa da Messi kan yiwuwar dawowarsa gida.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da zuba ido kan inda zai koma domin ci gaba da buga wasa a zangon kwallon kafa na shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel