Gwamnatin Buhari Ta Zargi Peter Obi Da Laifin Cin Amanar Kasa

Gwamnatin Buhari Ta Zargi Peter Obi Da Laifin Cin Amanar Kasa

  • Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al'adu na Najeriya ya zargi Mista Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour da mataimakinsa Datti Ahmed da cin amanar kasa
  • Mohammed ya bayyana hakan ne a Amurka yayin da ya kai wata ziyarar aiki don tattaunawa da kafafen watsa labarai dangane da babban zaben 2023 da aka kammala a baya-bayan nan
  • Ministan ya ce ba dai-dai bane bayan Obi ya tafi kotu yana kallubalantar sakamakon zaben ya kuma koma gefe guda yana tunzura magoya bayansa suna cewa idan har aka rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu, dimokradiyya ta zo karshe a Najeriya

Washington DC - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gargadi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Mista Peter Obi, kada ya tunzura mutane su tada rikici kan sakamakon zaben shugaban kasa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yes Daddy', Dan Majalisar Kano Ya Kwaikwayi Peter Obi Bayan Ganawa Da Kwankwaso

Alhaji Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al'adu, ya yi wannan gargadin a Washington DC, yayin tattaunawarsa da wasu kafafen watsa labarai na kasa da kasa a ziyarar aiki da ya kai.

Lai Mohammed
Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al'adu Ya Zargi Obi Da Datti Ahmed da Cin Amanar Kasa. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ta rahoto cewa ministan ya tafi Washington ne don ganawa da kafafen watsa labarai da kungiyoyin kwararru game da zaben 2023 da aka kammala.

NAN ta kuma rahoto cewa kawo yanzu ministan ya tattauna da “Washington Post”, Voice of America, Associated Press da Foreign Policy Magazine.

Ba dai-dai bane Obi ya tafi kotu sannan ya koma gefe yana tunzura magoya bayansa - Lai Mohammed

Yayin tattaunawar da kafafen watsa labaran, ministan ya ce ba dai-dai bane a bangare guda Obi ya tafi kotu don neman hakinsa kan zaben amma kuma ya rika tunzura mutane su tada rikici.

Kara karanta wannan

Hirar Waya Da Aka Bankado: Babban Faston Najeriya Bishop Oyedepo Magantu Kan Tattaunawarsa Da Obi

Ya ce:

"Ba zai yi wu Obi da mataimakinsa Datti Ahmed su rika yi wa yan Najeriya barazanar cewa idan aka rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na APC a ranar 29 ga watan Mayu, zai zama karshe dimokradiyya a Najeriya. Wannan cin amanar kasa ne. Ba zai yi wu ka rika gayyatar tada kayan baya ba, kuma wannan shine abin da suke yi.
"Kalaman Obi na mutum ne wanda ya yanke kauna, ba mutum ne da ya yarda da dimokradiyya kamar yadda ya ke ikirari ba."

Obi ya yi kus-kus da tsohon shugaban kasa Obasanjo a filin tashin jiragen saman Anambra

A baya kun ji Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ya hadu da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a Awka, jihar Anambra.

Obi ya rubuta a shafinsa na Twita wacce Legit.ng ta gani yana cewa ya yi murnar samun daman tattaunawa da Obasanjo.

Kara karanta wannan

Mazan jiya: Hotunan gidan Tafawa Balewa sun jawo martani mai daukar hankali a intanet

Asali: Legit.ng

Online view pixel