Kaman Almara: Wani Dan Najeriya Ya Yi Tafiya Kan Kwai Ba Tare Da Sun Fashe Ba, Bidiyon Ya Yadu

Kaman Almara: Wani Dan Najeriya Ya Yi Tafiya Kan Kwai Ba Tare Da Sun Fashe Ba, Bidiyon Ya Yadu

  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun nuna mamaki kan bidiyon wani dan Najeriya da ke tafiya akan kiras din kwai
  • Duk da yadda ya saki nauyinsa akan kiras din, babu ko daya a cikin kwan da ya fashe kuma haka ya janyo muhawara akan bidiyon
  • Matashin ya na shirya kiras din ne a motar daukar kaya kuma ya zama sai ya taka kwan kafin ya jera

Abu ne sananne cewa kwai ba shi da kwari kuma zai iya fashewa idan ya ji matsi.

Sai dai, wani bidiyo ya janyo cece-kuce a yanar gizo akan rashin kwarin kwai. Bidiyon ya nuna wani yadda wani matashi dan Najeriya ke hawa lodin kiras yana tsani da su.

Tafiya kan kwai
Wani Dan Najeriya Ya Yi Tafiya Kan Kwai Ba Tare Da Sun Fashe Ba, Bidiyon Ya Yadu. Hoto: @mufasatundeednut
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan matashi ya ketare iyakar kimiyya bayan da masu amfani da kafafen sada zumunta su ka fara dawo da abun da suka koya a makaranta kan dalilin da ya hana kwan fashewa.

Ya jera kiras din kwai daga gidan gona zuwa motar daukar kaya da zata raba su wurare.

Bidiyon ya nuna yadda ya ke rike da wasu kiras din ya na tafiya zuwa inda motar ta ke.

Daga nan, sai ya hau bayan motar ya kuma hau kan shiryayayyun kiras layi biyu don ajiye wanda ya dauko. Kwata kwata kwan bai fashe ba yayin da ya ke tafiya.

Ga martani daga kafafen sada zumunta

@mufasatundeednut na cewa:

"Tambayata shi ne, me yasa kwan bai fashe ba?"

Sharhin @papiijameh:

"Ba shi da abin da ya ke fasa kwai."

@officialmajoyorspeaks ya ce:

''Kwan da aka jera a tsaye ba ya fashewa? In ka na so ka yada da shirmen da na rubuta, kai ka sani."

Sharhin @naijatweets:

"Kwan da aka shirya da kyau daidai ta sama na da wahalar fashewa idan nauyi daya aka sanya."

Ra'ayin @priscillia_Oluchi

"Bature ya ce me? Adadin abu (kwai) idan aka tattara waje daya za su iya jure nauyin saboda dokar maganadisu (gravity). Kar a tambayi me na rubuta, ban ci komai ba".

@morgancol4 na cewa:

"Kwan diragon ne, tsohuwa ce tayi! Aljanu sun kusa mamayemu!!!"

@harry_walter123 ya yi bayani:

"Kimiyya mai sauki..........barin kwan mafi kwari shine sama da kasa, musamman tsinin sama. Saboda haka idan akara shirya kwan a kiras aka tsaya, kwan za su ji nauyi daya kuma haka zai hana kwan fashewa kuma kiras din ya taimaka. Kamar har yanzu na dan iya boko fa".

Ga bidiyon a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel