Portable Ya Garzaya Masallaci Kai Tsaye Don Yin Sallah Bayan Yan Sanda Sun Sako Shi, Bidiyon Ya Bazu

Portable Ya Garzaya Masallaci Kai Tsaye Don Yin Sallah Bayan Yan Sanda Sun Sako Shi, Bidiyon Ya Bazu

  • A karshe, Portable ya shaki iskan yanci a ranar 3 ga watan Afrilu bayan ya cika ka'idojin belinsa da kotu ta saka
  • Abin farin ciki ga magoya bayansa, mawakin ya dawo gida cikin annushuwa da wasa kamar yadda aka saba ganinsa, kuma suka yi ta binsa suna murna
  • An ji Portable na cewa yana son ya shiga masallaci da ke kusa da shi domin ya yi sallah

Mawakin Najeriya Portable ya sha gwagwarmaya a baya-bayan nan, amma hakan bai hana shi nuna irin halayensa da ya saba ba bayan dawowa gida.

Bayan cika ka'idojin belinsa da kotu ta saka, an kyalle mawakin ya koma gida, kuma dawowarsa unguwa ya faranta wa magoya bayansa rai.

Portable
Bidiyon Portable Ya Shiga Masallaci Don Yin Sallah Bayan Yan Sanda Sun Sako Shi. Hoto: @onlyinnigeria
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

"Kan 300k": Yadda Uba Ya Gwada 'Yarsa Don Ya Gane Ko Tana Taba Sana'ar Karuwanci a Makaranta

A wani bidiyon da ya bazu a dandalin sada zumunta, an hangi wasu matasa sun ruga da gudu suna bin Portable a kusa da wani masallaci.

Wasu cikin matasan suna ta murnar dawowarsa, kuma mawakin cikin farin ciki ya fada musu yana son ya yi sallah kafin ya shiga masallaci.

Magoya bayan mai wakan Zazu din sun yi kokarin daukan hotonsa yayin da ake hayaniyar maraba da shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun yi martani kan bidiyon Portable a intanet

evebawuro:

"Ya dawo Zoo din"

alahaja_armanii:

"Jarumi! Shin ba za ka yabi Ubangiji ba! Akoi grace!"

_rhowdah:

"Bayansa. Me ya samu bayansa?"

joeyatabo:

"Duk wadannan da suka binsa suna bada gudunmawa cikin matsalar."

muyensky:

"Mutumi na .... Ina fa dan son wannan gayen."

oz_dami:

"Ni kawai ina son portable."

two_sevenj:

"Ina son kazar-kazar dinsa"

dgmetor_ehis:

"Sabon jarumin gari a cikin laka"

_feyi01:

"Masu tsaron ka sun gaza kare ka a baya, birkitancen yaro."

Kara karanta wannan

An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

3bchops:

"Oga baboon ya dawo."

Bidiyon Mage Ta Yi Tsalle Ta Dare Kan Liman Yayin Da Ya Ke Jan Sallah Ya Bayar Da Mamaki

Bidiyon wani muzuru ko mage da ta dare kafar wani limamin yayin da ya ke jan sallar jami'i ya ba wa mutane a dama mamaki.

Kamar yadda aka gani, magen ta dare kafar limamin shi kuma ya cigaba da kira'a yana jan sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel