Uba Ya Gwada ‘Yarsa Don Ganin Ko Tana Taba Sana’ar Karuwanci, Ya Ba Ta Mamaki a Bidiyo

Uba Ya Gwada ‘Yarsa Don Ganin Ko Tana Taba Sana’ar Karuwanci, Ya Ba Ta Mamaki a Bidiyo

  • Wani uba ya dauki wata matashiya mai kirkirar bidiyo aiki domin su gwada ko diyarsa na yin sharholiya a makaranta
  • Ya boye a wajen da za a yi mata gwajin inda ya zuba ido yana kallo yayin da aka baiwa diyarsa damar kwana da wani kan kudi N300k
  • Abun da ya faru a gaba ya tsuma zukatan mutane da dama yayin da mutumin ya fito daga inda ya boye sannan ya baiwa diyar tasa mamaki

Wani dan Najeriya ya baiwa diyarsa tukwicin kudi da sauran abubuwan karfafa gwiwa bayan ya yi mata gwajin kwanciya da wani kan N300k.

Da yake zantawa da Shuga Plum, wata mai ai kirkirar bidiyo kafin gwajin, mutumin ya ce ya ga yadda maza ke daukar kananan yara don haka yake son tabbatar da irin rayuwar da diyarsa ke yi a makaranta.

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Ya Gwangwaje Wani Tsoho Mai Tura Baro Da Sha Tara Ta Arziki, Bidiyon Ya Tsuma Zukata

Uba ya shiryawa diyarsa gadar zare
Uba Ya Gwada ‘Yarsa Don Ganin Ko Tana Taba Sana’ar Karuwanci, Ya Ba Ta Mamaki a Bidiyo Hoto: @shuga_plum
Asali: TikTok

Ya isa wajen gwajin sannan ya nemi wuri ya boye. Ga farin cikinsa, diyarsa mai suna Chidinma, ta isa wajen, ta ki amsa tayin sannan ta bayyana cewa ita bata taba tarawa da wani 'da namiji ba.

Uban wanda ya cika da alfahari ya fito daga wajen da ya boye sannan ya jinjinawa diyar tasa cikin daga murya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A nan take, ya baiwa matashiyar kyautar miliyan daya, ya yi mata alkawarin mayar da ita Canada da mota. Uba da diyar tasa suka rungume junansu yayin da suke farin ciki.

Bidiyon na TikTok ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Idris Bawa ya ce:

"Amin. Diyar albarka ce. Allah ya ci gaba da kareta, ya daukaka ta sannan ya sa ta zamo farin ciki ga al'umma."

Kara karanta wannan

An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

@Big Boy ya ce:

"Shuga plum yanzu an sanki sosai watakila sun san ki don haka ba za su ba da kai bori ya hau ba a nan gaba a bari wani ya yi mu gani."

@enenduelcee ta ce:

"Shiri mafi kyau. na taya uba da diyar da dangin farin ciki. Wannan matar aure ce ta gari. tarbiya mai kyau."

@dembacham9141 ya ce:

"Yarinya yar kirki Allah ya albarkaci iyayenki saboda iyayen kirki ne."

An kama malami yana cika tumbi da abincin dalibarsa a bidiyo

A wani labari na daban, mun ji cewa bidiyon wani malami ya karade shafin soshiyal midiya inda aka gano shi yana cika tumbinsa da abincin daya daga cikin dalibansa a makaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel