Ko Gezau: Mage Ta Yi Tsalle Ta Faɗa Kan Liman Yayin Da Yake Jan Sallah, Bidiyon Ya Bayar Da Mamaki

Ko Gezau: Mage Ta Yi Tsalle Ta Faɗa Kan Liman Yayin Da Yake Jan Sallah, Bidiyon Ya Bayar Da Mamaki

  • A wani bidiyo da shafin kafar watsa labarai ta TRT Hausa ta wallafa a shafinta na Tuwita an ga yadda wata mage ta daka tsalle ta fado kan Liman yayin da yake jan jama’a Sallah
  • Lamarin ya faru ne a Masallacin Abubakar al Siddiq da ke wani birni mai suna Bordj Bou Arreridj da ke kasar Algeria kamar yadda kafar TRT ta rawaito
  • Ko kadan limamin Masallacin bai razana ko tsorata ba yayin da magen ta fado masa babu zato babu tsammani

Mage (mace) ko kuma Muzuru (namiji) na daga cikin dabbobin da mutane da yawa suka aminta dasu har suke ajiyewa a gidajensu domin debe musu kewa. Sai dai, duk da haka har yanzu akwai wasu mutane dake matukar tsoron mage, wasu ko gidan da ake kiwon mage basa iya ziyarta saboda tsananin tsoron mage.

Kara karanta wannan

Rashin daraja: Bidiyon dalibai sadda suke yiwa lakcara isgili don ya zo da balkwatacciyar mota

Koda mutum baya jin tsoron dabbobin da ake ajiyewa a gida, a mafi yawan lokuta mutum kan razana tare da firgita idan irin wadannan dabbobi suka fado kansa ko kuma suka yi motsi ko kuka babu zato babu tsammani.

Mage ta hau kafadar limami
Mage Ta Yi Tsalle Ta Faɗa Kan Liman Yayin Da Yake Jan Sallah, Bidiyon Ya Bayar Da Mamaki. Hoto: @trtafrikaHA
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sabanin irin wadannan mutane dake razana ko firgita idan dabbobin da suke kiwo sun fado kansu ko sun yi kuka babu tsammani, Limamin Masallacin Abubakr al Siddiq da ke birnin Bordj Bou Arreridj da ke kasar Algeria ya bawa mutane mamaki saboda jarumtarsa.

Ko gezau limamin bai yi ba a yayin da wata mage ta daka tsalle ta fado kansa a yayin da yake cikin rera kira’ar Alqur’ani mai girma a lokacin da yake jan jama’a sallah.

A faifan bidiyon da shafin watsa labarai na TRT da ke kasar Turkiyya ta wallafa a shafinta na Tuwita (@trtafrikaHA) za’a iya ganin yadda magen ta yi tsalle ta haye kan kafadar Malam Liman kafin daga bisani ta hau tsakiyar kansa tare da gangarowa zuwa kan kirjinsa.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

Ga bidiyon a kasa:

Martanin wasu masu amfani da Twitter

Wani daga cikin wadanda suka yi martini a kan faifan bidiyon ya bayyana cewa dadin kira’ar karatun Malam Liman ne ya jawo magen zuwa masallacin, ma’ana shaukin karatun Liman ne.

@Deluwa ya ce:

"Akwai alamar shakuwa tsakanin Malam Liman da wannan Mage/Muzuru."

@im___sultan cewa ya yi:

"Mage ma fa kenan, ta shiga shauki da jin karatun Alkurani mai Girma."

@Abdul_Kyauta ya yi martani da cewa:

"Subuhanallah"

Da legit.ng Hausa ta tuntubi wani malamin addini mai suna Alhaj Idi Burtulan ya ce babu wata dabba da zata firgita mutumin da ya tsaya a gaban ubangiji da zuciya daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel