Kafin a Rantsar da Shi, Kungiyoyin NLC da TUC Sun Shiga Ynkurin Yi Wa Tinubu Tutsu

Kafin a Rantsar da Shi, Kungiyoyin NLC da TUC Sun Shiga Ynkurin Yi Wa Tinubu Tutsu

  • Shugabannin Kungiyoyin NLC da TUC sun nuna ba za su goyi bayan karin farashin man fetur ba
  • Ma’aikatan Najeriya sun ba Bola Tinubu shawara cewa gwamnatinsa ta gyara matatun danyen mai
  • ‘Yan kwadago sun nuna ba za su yi na’am da janye tallafin fetur idan ba za a farfado da matatu ba

Abuja - Kungiyoyin NLC da TUC na ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa a Najeriya, sun yi magana a kan batun janye tallafin man fetur da za ayi a bana.

Punch ta rahoto kungiyoyin su na masu cewa za su goyi bayan dakatar da tallafin fetur ne idan gwamnatin Bola Tinubu za ta gyara matatun mai.

Muddin ba za a farfado da matatun danyen mai da ake da su, sannan a kafa wasu kananu ba, kungiyoyin sun ce za su fito su shirya zanga-zanga.

Kara karanta wannan

To fah: INEC ta yi hayar wasu manya, fitattun lauyoyi 9 a Najeriya don kare sakamakon zaben 2023

Ministar tattalin arziki, tsare-tsare da kasafin kudi, Zainab Ahmed ta ce daga Mayun 2023, gwamnati ba tayi wani tanadi na rage farashin fetur ba.

Ma'ajin NLC ta bada sharadi

Daya daga cikin shugabannin NLC na kasa kuma shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi, Hakeem Ambali ya bayyana matsayarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A matsayinsa na ma’aji, da aka zanta da shi kwan nan, Kwamred Hakeem Ambali ya ce har gobe kungiyar NLC ba ta goyon bayan a janye tallafin.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima a taro Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kamar yadda yake fada, ya zama dole gwamnati ta gyara matatun da ke tace danyen fetur, ya ce bai dace a rika shigo da mai daga kasashen ketare ba.

Kan TUC da NLC daya

Haka zalika shugaban kungiyar malaman makaranta a Najeriya, Titus Amba ya nuna su na tare da uwar kungiyar kwadago dari bisa dari a kan batun.

Kara karanta wannan

Mazan jiya: Hotunan gidan Tafawa Balewa sun jawo martani mai daukar hankali a intanet

Mataimakin shugaban TUC kuma shugaban kungiyar manyan ma’aikata, Tommy Etim ya ce akwai bukatar gwamnati mai zuwa tayi gyara da wuri.

Vanguard ta rahoto Tommy Etim yana cewa akwai yaudara a tsarin tallafin man fetur, ya ba gwamnatin Bola Tinubu shawarar ta gyara matatun mai.

Ana ganin hakan zai jama’a su samu ayyukan yi, kuma a daina fama da karanci da wahalar mai.

Menene matsayar Asiwaju Bola Tinubu?

A baya an samu rahoto cewa Asiwaju Bola Tinubu ya fada, kuma ya nanata cewa gwamnatinsa za ta cire tallafin man fetur da zarar ya shiga ofis.

‘Dan takaran shugaban kasan na APC a 2023 yana ganin talaka bai cin moriyar kudin tallafin da ake biya, ya ce masu kudi ne suke amfana da tsarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel