‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Dage Sai Ya Cire Tallafin Fetur Idan Ya Gaji Buhari

‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Dage Sai Ya Cire Tallafin Fetur Idan Ya Gaji Buhari

  • Asiwaju Bola Tinubu ya fada, kuma ya nanata cewa gwamnatinsa za ta cire tallafin man fetur
  • ‘Dan takaran shugaban kasan na APC yana ganin talaka bai cin moriyar kudin tallafin da ake biya
  • Tinubu ya ce masu kudi ne suke amfana da tsarin don haka zai soke shi, sai ayi wani abin da kudin

Kano - Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, ya sake jaddada niyyar janye tallafin man fetur a Najeriya.

The Nation ta ce ‘dan takaran ya yi wata hira da gidan rediyon Freedom bayan dawowarsa daga Umrah, a nan ya tabbatar da zai soke tallafin fetur.

Asiwaju Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta jurewa tsarin tallafin man fetur ba domin hakan bai amfanar da talaka, sai dai ma ya jefa shi a kangi.

Kara karanta wannan

2022: Wasu manyan abubuwa 10 da suka faru a 2022, sun ja hankalin jama'a a duniya

‘Dan takaran ya ce gwamnatocin baya da suka rika biyan tallafin, asara dukiyar kurum suka yi, ya ce kyau a kashe kudin a kan abin da ake bukata.

Zan kawo karshen lamarin - Bola Tinubu

“Zan tabbatar na kawo karshen barnar, a karkatar da kudin zuwa ga ainihin jama’an da suke da bukatarsa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Bola Tinubu

A rahoton The Cable, tsohon Gwamnan na jihar Legas ya ce attajirai ne suke amfana da wannan tsari da aka saba da shi na biyan tallafin fetur a kasar nan.

‘Dan Takaran APC
‘Dan Takaran APC, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

An fito da tsarin ne domin talaka ya samu sauki wajen sayen fetur, amma akasin haka ake gani, saboda haka Tinubu ya ce gwamnati za ta cire hannunta.

Akwai bukatar ayi gyara a harkar mai

Vanguard ta ce wannan yana cikin manufofin da ‘dan takaran ya gabatar, da bakinsa kuma ya fadawa ‘yan Najeriya dole sai an yi gyara a bangaren man fetur.

Kara karanta wannan

An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

A ra’ayin Tinubu, a maimakon a rika kashe kudi domin fetur ya yi araha, zai fi kyau a karkatar da dukiyar da ake batarwa wajen kula da harkar kiwon lafiya.

Tinubu ya yi karin haske da kyau

A lokacin da ya yi magana kwanaki, Tinubu ya ce zanga-zangar mutane ba za ta hana a janye tallafin ba, hakan ya sa wasu suka yi masa muguwar fassara.

‘Dan siyasar ya yi karin haske cewa bai nufin hana mutane neman hakkinsu domin shi ma ya yi zanga-zanga a baya, ya ce dole sai ya tuntubi jama’a tukuna.

APC ta rabawa kiristoci abinci

An ji labari shugaban kwamitin neman zaben Tinubu/Kashima a Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya yi rabon buhunan shinkafa 250 da buhunan masara 750.

Shugaban CAN a Zamfara, Ahmad Haruna da Eze-Igbo, Egbuna Obijiaku sun karbi kayan abincin, sun yi alkwarin za a rabawa masu bukata, kuma ayi addu’a.

Kara karanta wannan

A zatona na mutu: Tsohon Gwamnan da 'yan bindiga suka farmaki ayarinsa ya magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel