Kotun Koli Ta Kori Karar da Tsohon Minista Emeka Ya Shigar a Kan Zargin Tinubu da Atiku da Sayen Kuri’u

Kotun Koli Ta Kori Karar da Tsohon Minista Emeka Ya Shigar a Kan Zargin Tinubu da Atiku da Sayen Kuri’u

  • Kotun koli ya yi waje da karar da aka shigar kan batun da ya shafi zaben fidda gwanin shugaban kasa na shekarar da ta gabata
  • Kotun ya ce, Emeka, tsohon ministan Buhari da kungiya mai zaman kanta basu da ikon shigar da irin wannan karar
  • An yi zabe a Najeriya, Bola Tinubu ya lashe zabe, lamarin da ya tunzura Atiku da Obi, inda suka tafi kotu neman adalci

FCT, Abuja - Kotun koli a Najeriya ya yi watsi da karar da Chukwuemeka Nwajiuba, tsohon karamin ministan ilimi a Najeriya ya shigar na neman haramtawa Bola Tinubu da Atiku Abubakar yin takara a zaben bana.

Hukuncin na zuwa ne a ranar Alhamis 30 ga watan Maris a wani zaman kotu da mai shari’a Inyang Okoro ya jagornata, inda ya bayyana yin watsi da karar, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: An kafa tarihi, kasar Turai ta nada Firayinminista Musulmi a karon farko

Kafin yin watsi da ita, Emeka ya bayyana bukatar janye karar bayan da kotun ya bayyana kuskuren da ya yi na shigar da karar ba a daidai lokacin da ya dace ba.

An kori karar da ke neman hana Tinubu da Atiku takara
Atiku Abubakar da Bola Tinubu | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yadda aka shigar da karar tun farko

Emeka da Rights for All International (RAI) sun shigar da kara a tun farko a gaban babban kotun tarayya, inda suka nemi a watsar da tsarin da ya kawo Tinubu da Atiku a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa, Punch ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun bayyana zargin cewa, dukkan ‘yan takarar biyu sun yi amfani da kudi ne wajen sayen deliget-deliget na zaben fidda gwanin da ya basu nasarar tsayawa takarar shugaban kasa a APC da PDP.

Mai shari’a Inyang Ekwo na babban kotun tarayya ya yi watsi da karar a baya, inda yace masu shigar da karar basu da ikon shigar da irin wannan karar.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi, Festus Keyamo Ya Bayyana

A cewarsa, a dokance kungiyar tallafawa al’umma irinta RAI mai zaman kanta ba ta da 'yancin shigar da kara kan batun da ya shafi siyasa.

Kotun daukaka kara ya yi watsi da batun

Daga nan ne suka ki amincewa da hukuncin kotun, inda suka dunguma zuwa kotun daukaka kara.

A can ma bata sauya zane ba, kotun na daukaka kara ya yi watsi da batun saboda rashin daidaito da ikon shigar da karar.

Yanzu dai komai ya kankama, an yi zabe Tinubu ya lallasa Atiku da Obi, gashi an kori karar Emeka.

Amma da sauran rina a kaba, domin Atiku da Obi sun ce ba za su amince da sakamakon zaben ba, za su kai kara gaban kotu.

A halin da ake ciki, ana zargin wasu ‘yan siyasa da kitsan hanyar kafa gwamnatin wucin gadi a kasar, lamarin da ya jawo martanin APC da PDP.

Kara karanta wannan

2023: An Kai Karar Hadimin Tinubu a Babban Kotun Duniya Saboda Bakaken Kalamai

Asali: Legit.ng

Online view pixel