Ku Bayyana Sunaye Sannan Ku Kame Masu Son Kafa Gwamnatin Wucin Gadi, APC, PDP Ga DSS

Ku Bayyana Sunaye Sannan Ku Kame Masu Son Kafa Gwamnatin Wucin Gadi, APC, PDP Ga DSS

  • Shugabancin jam’iyyar APC da jam’iyyar PDP sun tura sako mai muhimmanci ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS)
  • Jam’iyyun biyu sun nemi hukumar tsaron da ta bayyana sunayen ‘yan siyasar da ke son kafa gwamnatin wucin gadi tare da kama su
  • Dukkansu suna kan ra’ayin cewa, kafa gwamnatin wucin gadi a kasar ya saba da kundin tsarin mulki don haka akwai bukatar daukar mataki

Tawagar kamfen takarar shugaban kasa na APC da PDP sun bayyana bukatar DSS ta dauki mataki kan wasu baragurbin ‘yan siyasa a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar tsaro ta DSS ta gano cewa, akwai wasu ‘yan siyasa a Najeriya da ke shirin kafa gwamnatin wucin gadi kafin rantsar da Bola Tinubu.

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Laraba cewa, jam’iyyun sun ce kafa gwamnatin wucin gadi ya saba doka, don haka a gaggauta bayyana sunayen ‘yan siyasan da ke shirin hakan tare da kwamushe su.

A kamo duk masu son kafa gwamnatin wucin gadi, APC da PDP ga DSS
Shugaban APC na kasa da na PDP na kasa | Hotuna: Abdullahi Adamu, Umar Damagum
Asali: Facebook

Sun kuma yi magana mai daukar hankali game da ikrarin na DSS kan masu son kawo tsaiko ga kafa sabuwar gwamnatin Tinubu, rahoton TheCable.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayanin DSS na gano masu kitsa yadda za a kafa gwamnatin wucin gadi

A tun farko, hukumar DSS ta ce, ta tabbatar da akwai wasu ‘yan siyasa da ke kokarin ganin sun kafa gwamnatin wucin gadi kafin a rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Idan baku manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sauka a watan Mayu, inda zai mika wa zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Sai dai, har yanzu akwai wasu ‘yan siyasan da ke yawan kira ga Buhari da kada ya amince ya mika mulki ga Tinubu saboda a ra’ayinsu an samu aringizon kuri’u a zaben da aka yi.

Rikicin cikin gida a PDP ya kazanta

A bangare guda, tun bayan faduwa a zaben shugaban kasa jam’iyyar PDP ta dare, inda ake ci gaba da samun tsaiko a shugabancinta.

A makon nan ne aka samu labarin yadda jam’iyyar ta dakatar da shugabanta na kasa, Dr Iyorchia Ayu.

A bangaren tawagar kamfen din shugaban kasa na PDP, ta ce dakatar da Ayu ya saba doka, akwai bukatar wasu abubuwa da za a yi a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel