Hattara Masu Neman Aiki: Ga Yadda Zaku Nemi Aikin Jami'an Tsaro Na Ɓangare 3 da Akeyi Yanzu Haka

Hattara Masu Neman Aiki: Ga Yadda Zaku Nemi Aikin Jami'an Tsaro Na Ɓangare 3 da Akeyi Yanzu Haka

  • Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa tana ɗiban sabbin ma'aikata
  • Haka ita ma "Rundunar sojin Najeriya ɗaukar ma'aikata data keyi akai akai" don cike gurbi
  • Rundunar sojin Najeriya ta Ruwa itama tana ɗaukan nata ma'aikatan, a gwada, a dace

A lokuta da dama, akan yi fafutukar ɗaukan ma'aikata, amma mutane basu sani.

Hakan yakan sanya a rasa damar samun ayyukan ga matasa masu hazaƙa da cancanta.

Legit.ng ta kawo ayyukan sa wasu ɓangarori guda 3 na sashin tsaro da yanzu haka suke ɗiban ma'aikata.

Nigeria army
Hattara Masu Neman Aiki: Ga Yadda Zaku Nemi Aikin Jami'an Tsaro Na Ɓangare 3 da Akeyi Yanzu Haka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. NDLEA: Itace ce hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa wacce aka fi sani da NDLEA.

Hukuma ce da take kula da kuma yaki da fataucin duk wata kwaya mai cutarwa da take sa maye tare da kare yan kasa daga yin marisa mai illa.

Waje ne mai kyau a batun aiki, kuma albashin su, yana da gwabi-gwabi.

Ga mai bukata zai iya nema musamman idan ana da kwalin makaranta daya hada da Sakandire, Diploma/NCE, ko Digiri/HND.

Za'a iya neman aikin nata a:

https://recruitment.ndlea.gov.ng/

NDLEA
Hattara Masu Neman Aiki: Ga Yadda Zaku Nemi Aikin Jami'an Tsaro Na Ɓangare 3 da Akeyi Yanzu Haka
Asali: UGC

Lokacin ƙarshe da za'a rufe ɗauka: Asabar, 8 ga watan A️frilu, 2023

2. Nigeria Army: Rundunar Zaratan sojin Najeriya da ta saba ɗaukar ma'aikatan ta akai akai, don cike gurbi masu ritaya da wadanda suka rigamu gidan gaskiya, suma sun bude shafin su na yanar gizo-gizo da masu bukata

Yana da kyau mai nema ya sani, rundunar sojojin Najeriya sun dade da soma ɗaukar jaruman zaratan Najeriya masu sha'awar bautawa ƙasa. Amma mutane da yawa basu sani ba.

A hanzarta a nema tanan

Za'a iya neman aikin anan:

https://recruitment.army.mil.ng/darrr

Kwanan watan da za'a tsaida ɗiban: 14 ga watan Afrilu, 2024.

Nigerin army
Hattara Masu Neman Aiki: Ga Yadda Zaku Nemi Aikin Jami'an Tsaro Na Ɓangare 3 da Akeyi Yanzu Haka
Asali: UGC

3. NAVY: Watau Rundunar Sojin Najeriya na Ruwa.

Kamar yadda suka saba suma suna diban ma'aikata, amma mutane da yawa basu sani ba.

Yadda Za'ai a nema

A shiga madanni na ƙasa:

https://www.joinnigeriannavy.com/application-guidelines/

Lokacin da za'a daina amsar masu neman aikin: 6 ga watan Mayu, 2023

Navy 2
Hattara Masu Neman Aiki: Ga Yadda Zaku Nemi Aikin Jami'an Tsaro Na Ɓangare 3 da Akeyi Yanzu Haka
Asali: Depositphotos

Kada a jira ace sai anjima, a nema yanzu sannan a nemi sa'a daga ubangiji madaukakin sarki.

Allah ya bada sa'a

Samu Wuri: Wata yar Najeriya Ta Koka Abisa Yadda Aiki Yayi Mata Yawa a Kasar Dubai

A yayin da ake kukan ba aiki a Najeriya, wata yar Najeriya kuka tasha a ƙasar dubai, badon komi ba sai don aikin da take ya ishe ta.

Ta wallafa vidiyon ne a kafar sadarwa ta zamani, Jaridar legit.ng kuma ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel