"Zan Koma Gida": Wata Yar Najeriya Ta Sharɓi Kuka A Bidiyo Mai Ratsa Zuciya, Ta Ce Ta Gaji Da Aiki A Dubai

"Zan Koma Gida": Wata Yar Najeriya Ta Sharɓi Kuka A Bidiyo Mai Ratsa Zuciya, Ta Ce Ta Gaji Da Aiki A Dubai

  • Wata budurwa yar Najeriya ta wallafa bidiyo a dandalin sada zumunta saboda damuwa kan sana'arta
  • A cewar matashiyar, ba ta san yadda za ta fada wa mahaifiyarta cewa ta gaji aiki a Dubai
  • Mutane da dama masu amfani da dandalin sada zumunta sun aika mata sakon fatan alheri da karfafa mata gwiwa kan matsalolin da ta ke fama da shi a Dubai

Wata budurwa yar Najeriya da ke aiki a Dubai ta koka kan cewa ta gaji da aiki a kasar a kafar sada zumunta.

A wani bidiyo da ta wallafa a TikTok da aka yi imanin a wurin aiki ta dauka, budurwar ta yi kuka a bidiyon, tana juyayin yadda za ta fada wa mahaifiyarta yadda ta ke ji game da aikin.

Yar Dubai
Ta yi kuka saboda aikinta. Hoto: @kweenranty
Asali: TikTok

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Yi Kuka Da Hawaye Saboda Rashin Saurayi, Bidiyon Ya Yadu

Da ta ke mayar da martani ga masu amfani da shafukan intanet, ta bayyana cewa ta shafe kimanin shekaru hudu a Hadaddiyar Daular ta Laraba. Amma, ba ta fayyace irin aikin da ta ke yi ba.

Bidiyon na ta na TikTok ya yadu, inda mutane da dama suka karfafa mata gwiwa kada ta karaya. Wasu sun sa ta fahimci cewa ta fi wasu da ke Dubai din na watanni amma ba su da aiki.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin masu amfani da dandalin sada zumunta

@user8328107030209 ya ce:

"Ka da ki sake kuka a kyamara yar uwa hakan bai yi kyau ba amma Allah ya taimake ki."

@ICH LIEBE DICH ya ce:

"Ina tausaya miki, Abu masu kyau ba su zuwa da sauki. Allah zai baki ikon jure wa."

@Gbadebo John ya ce:

"Sannu, muna da yawa a nan fa. Ki yi maneji kawai har sai kin yi shawara. Allah ya taimake ki."

Kara karanta wannan

Ina gamsar dasu: Bidiyon matar da ta auri maza 3, take rayuwa dasu a cikin gida daya

@Ifadatty ya ce:

"Na riga na fada mata amma idan ta natsu ba ta karaya ba, zan koma."

@Adebaby ya ce:

"Ki gode wa Allah kin samu aiki akwai wadanda sunyi watanni fiye da 17 a Dubai din amma ba su da aiki."

@Enitan Lexy ya ce:

"Ki yi hakuri, Allah ya karfafa miki gwiwa amma ka da ki karaya, ki cigaba da kokari."

@OSHUN GODDESS ta ce:

"Wasu lokutan muna iya shiga irin wannan halin amma tashi a cigaba da gwagwarmaya shine, ina kaunar ki sarauniya.
"Ina aika miki haske. Abubuwa za su warware daga karshe."

Murja Kunya: An sake zuwa kotu, Alkali ya ce a cigaba da tsare ta a gidan yari

A baya, kun ji cewa a ranar 16 ga watan Fabrairu, an sake gurfanar da Murja Ibrahim Kunya fitacciyar yar TikTok a kotun shari'ar musulunci da ke Filin Hoki a Kano.

Kara karanta wannan

“Zan Fasa Auren”: Kyakkyawa Amarya Ta Ajiye Kunya Ta Tika Rawa Iya Son Ranta a Wajen Bikinta, Bidiyon Ya Yadu

Asali: Legit.ng

Online view pixel