Canjin Kuɗi: Masu Garkuwa Sun Tafi Rabin Lokaci, Yan Bindiga Suna Hutu, Ngige

Canjin Kuɗi: Masu Garkuwa Sun Tafi Rabin Lokaci, Yan Bindiga Suna Hutu, Ngige

  • Ministan Kwadugo da rage zaman kashe wando, Chris Ngige, ya ƙara magana kan sauya fasalin takardun naira
  • Dakta Chirs Ngige, ya faɗi amfanin canjin kuɗin da CBN ya aiwatar tun daga kan yan bindiga, masu garkuwa da yan siyasa
  • Ya ce babban banki ya saki takardun kudi masu yawa domin rage radaɗin da 'yan Najeriya suka shiga cikin yan kwanaki kaɗan

Abuja - Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce canjin kuɗin da babban bankin Najeriya (CBN) ya bullo da shi ya haifar da ɗa mai ido.

Ministan ya ce sabon tsarin sauya fasalin naira N200, N500 da N1000 ya taka wa matsalar tsaro da sayen ƙuri'u a lokacin babban zaben 2023 da aka kammala birki.

Ngige.
Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige Hoto: channelstv
Asali: UGC

Ngige ya yi wannan jawabi ne a cikin shirin Channels tv mai suna Politics Today ranar Laraba. A kalamansa ya amince aiwatar da tsarin ya zo da tangarɗa mai wahala.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Sabuwar Rijiyar Mai Ta Jihar Nasarawa

A kalamansa ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tsarin baiwa mutane daɗi ba wajen ƙaƙaba musu shi, na yarda da wannan, amma tsari ne na gari? Kwarai tsari ne mai kyau. Tsarin ya zo da ƙuncin rayuwa amma yana da alfanu da yawa."
"'Yan siyasa sun rasa damar sayen kuri'a a kan layin zaɓe, ina zuwa wurin zaɓe kuma na san abinda na saba gani, wannan karon ba'a sayi kuri'u ba. Abun ba sauki a yanzu."
"Masu garkuwa kuma sun tafi hutun rabin lokaci ne ko sun tafi yajin aiki, ko kuma mu ce sun ja da baya daga aikata muggan laifuka. Yan bindiga kuma an taka musu birki."

Game da dakatar da zanga-zangar NLC kuwa, Ministan ya ce CBN ya saki ƙarin takardun naira ga yan kasa domin yaye musu ƙuncin da suka shiga nan da 'yan kwanaki.

Kara karanta wannan

Karin Shekara: Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Aike da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya Kafin Hawa Mulki

Hankalin Emefiele ya tashi kan zanga-zangar NLC

A wani labarin kuma Gwamnan CBN Ya Roki NLC Ta Janye Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Karancin Naira

Godwin Emefiele ya yi wannan roko ne a wurin ganawarsa da shugabannin NLC karkashin jagorancin ministan kwadugo, Chris Ngige.

Ya ce CBN ya ɗauki matakan da ya dace domin wadatar da takardun kuɗi a hannun jama'a kuma hakan ya sa bankuna suka yi aiki a ranakun karshen mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel