Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Albashin Ma'aikata

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Albashin Ma'aikata

  • Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi na ƙasa ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta amince da ƙarawa ma'aikata albashi
  • Mr Chris Ngige yace ƙarin na da muhimmanci ne duba da yadda abubuwa suka carke da tsada a ƙasar nan
  • Ministan ƙwadagon ya bayyana cewa amincewar shugaban ƙasa Buhari kaɗai ake jira a fara aiwatar da ƙarin albashin ga ma'aikatan ƙasar nan

Abuja- Ministan Ƙwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin albashi ga ma'aikatan ƙasar nan. Rahoton The Punch

Ngige ya bayyana hakan ne a daren ranar Laraba a wani shirin gidan talabijin na Channels Tv mai suna 'Siyasa a Yau'.

Buhari
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Albashin Ma'aikata Hoto: The Punch
Asali: UGC

Ministan ya bayyana cewa ƙarin albashin yana da muhimmanci duba da yadda tsadar abubuwa ta ƙaru a ƙasar nan, sai dai ya ƙara da cewa har yanzu shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, bai amince da kason da za ayi amfani da shi wajen ƙarin ba.

Kara karanta wannan

Malamin Addinin Musulunci Ya Dau Zafi Ya Bayyana Illar Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu

Ngige ya kuma yi nuni da cewa na sanya ƙarin albashin a cikin kasafin kuɗin shekarar 2023 sannan zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2023. Rahoton Channels Tv

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamnatin tarayya na son ba ma'aikatan gwamnati ƙarin albashi saboda yadda rayuwa ta ƙara yin tsada."
“A kwamitin shugaban ƙasa na albashi, mun yi wata huɓɓasa kan ma'aikatan gwamnati waɗanda suke akan tsarin biyan albashi na Consolidated Public Service Salary Structure (CONPSS) da wasu ma'aikatu dake akan tsarin CONPSS."
“Mun sanya wani kaso domin shugaban ƙasa ya amince da shi, a matakin kwamitin mu mun amince da shi. Mun ce zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2023."

"Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu Hadari Ce Babbba", Malamin Musulunci

A wani labarin na daban kuma, wani malamin addinin musulunci yayi gargaɗi kan masu ƙulla maƙarƙashiyar hana rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Karin Shekara: Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Aike da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya Kafin Hawa Mulki

Sheikh AbdulRahman Ahmad jagoran ƙungiyar Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria, yayi bayanin cewa ƙulla wannan maƙarƙashiyar na da matuƙar illa zaman lafiya da haɗin kan ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel