'Yan Bindiga Sun Raba Uwa Da 'Ya, Sun Halaka Wata Jaririya a Jihar Kaduna

'Yan Bindiga Sun Raba Uwa Da 'Ya, Sun Halaka Wata Jaririya a Jihar Kaduna

  • Miyagun ƴan bindiga marasa imani sun halaka wata sabuwar jaririya a ƙaramar hukumar Kagarko cikin jihar Kaduna
  • A kwanakin baya ne dai ƴan bindigan suka ɗauke mahaifiyar jaririyar lokacin tana ɗauke da juna biyu tare da mijin ta da kuma ɗiyar su
  • Ƴan bindigan bayan karɓar kuɗin fansa har sau biyu, har yanzu suna riƙe da ɗiyar iyalan a hannun su

Jihar Kaduna- Ƴan bindiga a ranar Lahadi sun halaka wata jaririyar matar da suka sace mai suna Shamsiya Mustapha, a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa matar aure, mijinta Mustapha da ɗiyar su mai suna Mahapuza Mustapha, ƴan bindigar sun sace su ne a gidan su dake ƙauyen Janjala cikin ƙaramar hukumar Kagarko s ranar 5 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

"Na Sama Da Mu Sun Karbi Tuhumar", 'Yan Sanda Sun Bayyana Halin Da Ake Ciki Game Da Shari'ar Ado Doguwa

Yan bindiga
'Yan Bindiga Sun Raba Uwa Da 'Ya, Sun Halaka Wata Jaririya a Jihar Kaduna Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sai dai, ƴan bindiga sun sako mijin matar auren, Mustapha, bayan sun karɓi kudin fansa har naira miliyan biyu (N2m) da sabon babur da kayan abinci.

Ƴan bindigan sun kuma riƙe matar auren mai ɗauke da juna biyu tare da ƴar ta inda suka buƙaci sai an sake basu wata miliyan biyun kafin su sake su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ta wayar tarho a ranar Laraba, wani ɗan'uwan matar, Yakubu Dati, yace matar ta haihu a hannun ƴan bindigan ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa bayan ƴan bindigan sun saki matar sun kuma rike ɗiyarta a hannun su inda suke nemi sai an basu naira miliyan ɗaya da rabi kafin su sake ta. Rahoton Naija News

"Kasan a lokacin da suka sace ta tare da mijinta da ɗiyar su, juna biyun ta ya kai wata bakwai. Ranar Lahadi shugaban ƴan bindigar ya kira iyalanta cewa su zo su ɗauke ta domin ta haihu." Inji shi

Kara karanta wannan

Matar Mark Zuckerberg, Attajiri Mai Kamfanin Facebook ta Haife Masa Ɗiya ta 3

Ya bayyana cewa lokacin da iyalan suka tuntuɓi shugaban ƴan bindigar dangane da jaririyar sai ya gaya musu cewa sun halaka ta.

"Abinda kawai iyalan matar suka yi shine sun je wani waje sun ɗauko ta zuwa gida inda yanzu haka ake duba lafiyar ta a wani asibitin kuɗi a Kagarko."
"Yanzu kawai babban tashin hankalin shine yadda za a haɗa miliyan ɗaya da rabi domin ganin yarinyar ta dake a hannun su an sako ta."

Bam Ya Tashi Da Shugaban Masu Hada Bam Na 'Yan Ta'addan Boko Haram

A wani labarin na daban kuma, shugaban masu haɗa bam na ƙungiyar Boko Haram, ya sheƙa barzahu bayan bam ya tashi da shi.

Awana Gaidam shine ya dasa bam ɗin da ya tashi yayin da yayi fata-fata da gangar jikin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel