Dara Taci Gida: Bam Ya Tashi Da Shugaban Masu Hada Bam Na 'Yan Ta'addan Boko Haram

Dara Taci Gida: Bam Ya Tashi Da Shugaban Masu Hada Bam Na 'Yan Ta'addan Boko Haram

  • Shugaban masu haɗa bama-bamai na ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram ya baƙunci lahira
  • Tantirin ɗan ta'addan ya mutu ne lokacin da wani bam da ya dasa ya tashi da shi a cikin dajin Sambisa
  • Mutuwar tantirin ɗan ta'addan ba ƙaramin koma baya bace ga ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram

Jihar Borno- Wani tanitirin ɗan ta'addan Boko Haram, Awana Gaidam, ya sheƙa barzahu a yayin da wani bam daya haɗa ya tashi da shi a dajin Sambisa.

Awana Gaidam mai shekara 39 a duniya yana ɗaya daga manya-manyan ƴan ta'addan Boko Haram, sannan yana daga cikin na gaba-gaba wajen haɗawa ƙungiyar bama-bamai masu fashewa.

Haram
Dara Taci Gida: Bam Ya Tashi Da Shugaban Masu Hada Bam Na 'Yan Ta'addan Boko Haram Hoto: Twitter/ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Awana yana da hannu wajen kai hare-hare bam kan dakarun sojojin Operation Hadin Kai yayin da suke rangadi akan hanyoyin Maiduguri zuwa Damboa, Bama zuwa Pulka da Bita da kuma Banki zuwa Darajamal.

Kara karanta wannan

"Na Sama Da Mu Sun Karbi Tuhumar", 'Yan Sanda Sun Bayyana Halin Da Ake Ciki Game Da Shari'ar Ado Doguwa

Majiyoyin sirri sun gayawa Zagazola Makama, wani masani mai sharhi kan lamuran tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa bam ɗin ya tashi da motar sa ne yankin Njumia da Arra cikin dajin Sambisa, a ranar 27 ga watan Maris, inda ko shurawa bai yi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyin sun bayyana cewa Awana ya sanya bama-bamai a wurare daban-daban kusa da sansanin sa domin bashi kariya, ashe bai sani ba kan shi tuggun da ya ƙulla zai ƙare ba, inda ɗaya daga cikin bama-baman yayi fata-fata da jikin sa.

Tun shekarar 2022, ƙungiyoyin ƴan ta'addan Boko Haram Islamic State of West Africa Province (ISWAP) sun kai hare-hare da bama-bamai fiye da sau 90 a yankin Arewa maso Gabas.

Ƴan ta'addan sun koma amfani da bama-bamai ne saboda matsin lambar da dakarun sojojin sama da na ƙasa suke musu da hare-hare ba ƙaƙƙautawa.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

Mutuwar Awana ba ƙaramin koma baya zai kawo ba ga ƙarfin kai hare-haren ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram.

Rikici Ya Barke a Tsakanin 'Yan Ta'addan ISWAP, Babban Kwamandan Ya Sheke Mataimakin Sa

A wani labarin na daban kuma, babban kwamandan ƙungiyar ISWAP, ya sheƙe mataimakin sa har lahira a wani sabon hargitsi da ya auku a tsakanin su.

Kwamandan ya halaka mataimakin na sa bisa zargin sakaci da aikin sa da yake yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel