Matar Mark Zuckerberg, Attajiri Mai Kamfanin Facebook ta Haife Masa Ɗiya ta 3

Matar Mark Zuckerberg, Attajiri Mai Kamfanin Facebook ta Haife Masa Ɗiya ta 3

  • Mark Zuckerberg shine mai kamfanin Facebook, Whatsapp, Instagram wanda a dunkule suka kira kamanin da Meta
  • Yanzu haka yana daya daga cikin jerin manyan attajirai na duniya wanda Jaridar Forbes take saki
  • Yana auren matar sa yar asalin kasar China, mai suna Priscilla Chan, auren nasu ya albarkatu da samun yaya guda 3 yanzu haka

Shahararren attajirin ɗan kasuwa dake Ƙasar Amurka da yake ɗaya daga cikin masu kuɗin duniya, Mark Elliot Zuckerberg ya samu ƙaruwa a ranar juma'a, 24 ga watan Maris na 2023.

Tunda da fari dai, matar attajirin mai suna Priscilla Chan ta dade da samun juna biyu wanda masoya da masu goyon baya suke ta zumuɗin ganin ranar da jarumar tasu zata haihu.

Priscilla Chan mata ga attajirin ta haifo santaleliyar lafiyayyar yarinya, da take kasancewa ta uku a wajen Zuckerberg.

Mark Zuckerberg
Matar Mark Zuckerberg, Attajiri Mai Kamfanin Facebook ta Haife Masa Ɗiya ta 3 Asali: Instagram
Asali: Instagram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mark Zuckerberg da yake uba ga ƴaƴa biyu kafin wannan haihuwa, yayi farin ciki sosai da samun ƙaruwar, domin kuwa saƙo gajere ya wallafa a shafin sa na Instagram a ranar juma'ar nan.

Mahaifin cike da alfahari, ya ɗauro hotunan cike da farin ciki a dandalin tare da wani ɗan gajeren sako kamar haka:

A cewar sa:

"Sannu da zuwa duniya, Aurelia Chan Zuckerberg! ƴar ƙarama, kema ɗaya ce daga ciki tarin ni'imomi."

Tuni dai masoya masu fatan Alkairi suka yi cincirindo a shafin nasa daya kasance tamkar gidan bikin suna daman taya shi murna.

Ga Kaɗan daga ciki:

Yodchatri:

"Muna taya ka murna Mark! Fatan kai da iyalin ka ku kasance cikin soyayya maras yankewa da farin ciki".

Themelindadavenport:

"Yarinya kyakkyawa! Tana da matuƙar kyau. Saƙon taya murna. Farin ciki nake domin ka da matar ka Priscilla"

Yes_we_can_cook:

"Sakon taya murna mai bamu hayar gida (Instagram)"

_Putriwid cewa yayi:

"Wannan yarinyar an haife tane ba tare da zatayi tunanin a ina zata samu kuɗi ba idan ta girma."

Saura dame, fatan mu dai daga wannan teburin, kowa Allah ya buda masa ya kuma bashi zuriya mai amfani.

Fayose Ya Yi Kakkausan Kalamai, Ya Fallasa Waɗanda Suka Jefa Najeriya Cikin Matsala.

Ayodele Peter Fayose tsohon gwamnan Ekiti yayi tonon silili daya girgiza masu saurare da bibiyar al'amuran yau da gobe.

Tsohon gwamnan yayi ikirarin cewa, yan siyasa, da duk wani mai madafar iko ya kamata a zarga akan yadda al'amuran yau da gobe suke ƙara lalacewa.

Jaridar Legit.NG ta ruwaito tsohon gwamnan na Ekiti na fadin cewa, tun zamanin 1978 , babu wani cigaba da kasar ke samu, banda tafiyar hawainiya da kuma tsayawa waje ɗaya da take ta faman yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel