'Yan Sanda Sun Yi Karin Haske Kan Tuhumar Da Ake Yiwa Ado Doguwa

'Yan Sanda Sun Yi Karin Haske Kan Tuhumar Da Ake Yiwa Ado Doguwa

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano tayi ƙarin haske kan tuhumar da ake yiwa shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai
  • Ana dai tuhumar Alhassan Ado Doguwa da laifin aikata kisan kai a ranar zaɓen 25 ga watan Fabrairu
  • Ƴan sandan sun bayyana cewa lamarin ya bar hannun su, inda lauyoyin gwamnati suka karɓi ragamar tuhumar a kotu

Jihar Kano- Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bayyana cewa tayi abinda ya dace dangane da zargin laifin kisan kai da ake yiwa shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa. Rahoton Leadership

Ana zargin ɗan majalisar da halaka wasu mambobin jam'iyyar he lawmaker New Nigeria Peoples Party (NNPP), a ƙaramar hukumar Tudun Wada, lokacin zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

An Tafka Magudi: Dan Takarar Gwamnan PDP Yaki Yarda Da Kaddara, Zai Kalubalanci Sakamakon Zabe a Kotu

Doguwa
'Yan Sanda Sun Yi Karin Haske Kan Tuhumar Da Ake Yiwa Ado Doguwa Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ƴan sandan na jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shine ya bayyana hakan inda yace kiran da shugaban jam'iyyar NNPP na ƙasa, Farfesa Rufai Alkali, yayi na ƴan sanda su gaggauta tuhumar Doguwa ya makaro, domin tuni suka miƙa lamarin ga fannin shari'a na jihar.

Ƴan sandan sun yi watsi da zargin da Alkali yayi na cewa suna yiwa lamarin tafiyar hawainiya, inda suka haƙiƙance cewa lamarin yanzu haka baya tare da su yana a hannun lauyoyin jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkali ya zargi ƴan sanda da rashin yin huɓɓasar da yakamata domin ganin an hukunta Doguwa bisa zargin da ake tuhumar sa da aikatawa. Rahoton Platinum Post

Kiyawa ya bayyana cewa:

“Bayan samun shawarwari ta fannin Shari'a, tuni aka miƙa lamarin zuwa kotu sannan aka haɗa musu da fayil ɗin tuhumar zuwa gare su."

Kara karanta wannan

“Karku Rantsar da Tinubu Domin Yin Hakan Ya Sabawa Dokar Tsarin Mulkin Najeriya” - Baba Ahmed

“Waɗanda a cikin ku suke cikin Kano suna da masaniya kan lamarin da abubuwan dake faruwa a kotu. Lamarin ya bar hannun ƴan sanda. Lauyoyin gwamnati sun karɓi ragamar tuhumar daga hannun ƴan sanda."

An Kai Karar Hadimin Tinubu a Babban Kotun Duniya Saboda Bakaken Kalamai

A wani labarin na daban kuma, an kai ƙarar wani hadimin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, gaban babban kotun duniya.

Ana tuhumar Bayo Onanuga da yin kalamai waɗanda ka iya sanyawa.rikici a ɓarke a tsakanin ƙabilun ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel