Mummunan Gobara Ta Tashi A Fitacciyar Kasuwa A Legas, Bidiyo Ya Fito

Mummunan Gobara Ta Tashi A Fitacciyar Kasuwa A Legas, Bidiyo Ya Fito

  • Wasu sassan daya cikin manyan kasuwanin jihar Legas, da ke Lagos Island, a halin yanzu yana ci da wuta
  • A cewar rahotanni, gobarar ya shafi wani plaza da ke kasuwar Balogun amma an tura jami'an hukumar kashe gobara daga bangarori biyu zuwa wurin da abin ya faru
  • Da ya ke martani, Jubril A. Gawat, hadimin gwamnan Jihar Legas kan sabuwar kafar watsa labarai ya bayyana cewa an shawo kan gobarar, an dakile yaduwarta zuwa wasu sassa

Jihar Legas - Gobara ta yi barna a fitacciyar kasuwar Balogun da ke Legas Island a ranar Talata, 28 ga watan Maris na 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta shafi wani rukunin shaguna inda ake sayar da takalman mata.

Kasuwar Balogun
Gobara ta lashe wani sashi na Kasuwar Balogun a ranar Talata, 27 ga watan Maris. Hoto: Jubril A Gawat
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

"Dama Na Faɗa" Gwamna Wike Ya Maida Martanin Kan Maye Gurbin Shugaban PDP Na Kasa

An tura jami'an hukumar kashe gobara su kai dauki a kasuwar

Jami'in hukumar kashe gobara daga bangarori biyu a Legas sun isa wurin don kashe gobarar.

An yi gobara daban-daban a kasuwar, inda aka rasa dukiyoyin miliyoyin naira.

Hadimin Gwamna Sanwo-Olu ya yi martani

Da ya ke martani kan afkuwar lamarin a shafinsa na Twitter, Jubril A. Gawat, @Mr_JADs, babban mataimaki na musamman (SSA) ga gwamnan jihar Legas kan sabuwar kafar watsa labarai, ya ce jami'an hukumar kashe gobara sun isa wurin.

A wani wallafa a Twitter da Legit.ng ta gani a ranar Talata, Gawat @Mr_JAGs ya rubuta:

Sanarwa kan gobara

"Hukumar kashe gobara da ceto na jihar Legas a halin yanzu suna can suna fafatawa da wuta a Kasuwar Balogun wacce ta shafi saman gidan mai bena biyar.
"Amma dai an yi galaba kan wutar don an dakile ta daga yaduwa."

Bidiyo ya fito

A bangare guda, wani mai amfani da shafin Twitter, D Obidient Son, @grayjoy69, ya wallafa bidiyon gobarar da ke faruwa a kasuwar Balogun.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hawaye sun kwaranya, fitaccen dan majalisa a wata jiha ya riga mu gidan gaskiya

Kalli bidiyon a kasa:

Wata mummunan gobara ta lakume shaguna guda 80 a babban kasuwar jihar Kano

A wani rahoton mai kama da wannan kun samu rahoton cewa mummunan gobara ta tashi a kasuwar Kurmi da ke birnin Kano a ranar Laraba 1 ga watan Maris.

Gobarar ta lakume shaguna a kalla 80 a cewa mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na jihar Kano, Saminu Abdullahi a wata sanarwa da ya fitar dangane da afkuwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel