"Ɗama Na Faɗa Maka Sai Ka Tafi" Gwamna Wike Ya Yi Murna da Maye Gurbin Ayu

"Ɗama Na Faɗa Maka Sai Ka Tafi" Gwamna Wike Ya Yi Murna da Maye Gurbin Ayu

  • Gwamnan jihar Ribas ya nuna farin ciki da maye gurbin shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu
  • A ɗazu jam'iyyar PDP ta sanar da maye gurbin Ayu da matamakin shugaba na arewa, Iliya Umar Damagun
  • Wannan na zuwa ne awanni bayan babbar Kotu a jihar Benuwai ta dakatar da Ayu daga kiran kansa shugaban PDP

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana gamsuwarsa game da kawar da shugaban jam'iyyar PDP ta ƙasa, Iyorchia Ayu.

PDP ta sanar da Umar Damagun a matsayin wanda zai maye gurbin Ayu a matsayin shugaban riko ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Wike da Ayu.
Gwamna Nyesom wike da Iyorchia Ayu Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wannan na zuwa ne kusan awanni 48 bayan kwamitin zartaswa na PDP a gundumar Igyorov, ƙaramar hukumar Gboko, jihar Benuwai, ya dakatar da tsohon shugaban nan take.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka Daga Kujararsa, An Maye Gurbinsa Nan Take

Gwamna Wike ya maida martani

Jim kaɗan bayan sanar da tsige Ayu, gwamna Wike ya yi murna da batun a wurin kaddamar da Titin Trans-Kalabari Phase 1, ƙaramar hukumar Degema, jihar Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kunga yadda Allah yake tafiyar da al'amura ko? Mutanen da suka jima suna kulla mana makirci an wayi gari su abun yake cutarwa a yanzu," inji Wike.

Gwamnan ya kuma gargaɗi masu murna da farin cikin sabon gwamnan Ribas da aka zaɓa su tuna har yanzu shi ke kan madafun iko har zuwa 29 ga watan Mayu.

Channels tv ta rahoto Wike na cewa:

"Don haka, idan ka yi ba daidai ba zan baɗa maka barkono. Kun ga yadda yaji na ya hana su zaman lafiya yanzu? Ba su ke wahala ba yanzu?"
"Ayu ya ce ba wanda ya isa ya dakatar da shi amma yau ya tattara komatsansa ya bar Ofis, yanzu muna da shugaban rikon kwarya. Na faɗa masa sai ka tafi, ko kana so ko baka so sai ka tafi."

Kara karanta wannan

Rikici Ya Kara Tsanani Bayan Umarnin Kotu, Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Shiga Tsaka Mai Wuya

"Lauyoyin da ke faɗa maka gunduma ba ta da hurumin dakatar da kai, NEC ce kafai ke da iko, ba zaka fahimta ba. Lokacin da ka zo, gunduma ce ta dakatar da Secondus har ka karɓi mulki."

Mutanen mazabar Ayu sun dira Sakatariyar PDP

A wani labarin kuma Masu Ruwa da Tsaki Na Mazaɓar Ayu Sun Mamaye Sakatariyar PDP Ta Kasa

Daga cikin tawagar har da mambobin PDP daga gundumar da ta dakatar da Ayu a jihar Benuwai, arewa ta tsakiya a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel