Mummunan Gobara Ta Kone Shaguna 80 A Babban Kasuwar Kano

Mummunan Gobara Ta Kone Shaguna 80 A Babban Kasuwar Kano

  • Wata gobara da ta tashi da asubar ranar Laraba ta lalata shaguna 80 a kasuwar kurmi da ke birnin Kano
  • Hukumar kashe gobara ta Jihar ta ce da samun rahoton ta tura jami'an ta wajen kuma sunyi nasarar dakatar da wutar daga cigaba
  • Wani dan kasuwar da abin ya shafa ya bayyana irin barnar da gobarar tayi tare addu'ar Allah ya kiyaye gaba

Jihar Kano - Wata gobara da ta tashi ranar Laraba 1 ga watan Maris a kasuwar Kurmi da ke Kano, ta lalata shaguna 80.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Taswirar Kano
Gobara ta lashe shaguna 80 a kasuwar kurmi a Kano. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Hukumar kashe gobara ta Kano ta magantu

Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin 5:23 na asuba daga wani Aliyu Alkasim game da tashin gobarar.

Kara karanta wannan

Yadda Gobara Ta Tashi a Kasuwar 'Monday Market' Da ke Maiduguri a Jihar Borno, Daruruwan Shaguna Sun Kone

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

''Yau, Laraba 1 ga watan Maris, 2023, dakin sa idon mu ya karbi kiran gaggawa da misalin 5:23 na asuba daga wani Aliyu Alkasim. Ya bada rahoton barkewar gobara a kasuwar Kurmi, da ke karamar hukumar Birnin Kano''

Abdullahi ya ce a take bayan karbar rahoton, hukumar ta tura jami'an ta wajen da abin ya shafa.

''Mun tuntubi jami'an mu daga ofisoshin da ke kwaryar birni. Da isar su wajen da misalin 5:27 na asuba, inda gobarar ya shafa ya kai kafa 160 X 100.''

Ya ce da kokarin jami'an su, hukumar tayi nasarar tseratar da shagunan kasuwar da dama kuma babu wanda yaji rauni ko ya rasa ransa.

Ya ce har yanzu ana binciken musabbabin gobarar.

Ya kuma bukaci al'umma da su dinga kashe kayan amfanin lantarki da kuma datse hanyoyin lantarkin idan ba a amfani da su a kuma guji amfani da wuta a cikin kasuwa.

Kara karanta wannan

EFCC Ta Kama Malamin Jami'ar Najeriya Da Tsabar Kudi N306k A Rumfar Zabe

Wani dan kasuwar da gobarar ta rutsa da shagonsa, ya bayyanawa Legit.ng Hausa cewa gobarar Allah ya takaita bata yi barnar da ta mamaye kasuwar gaba daya ba.

Dan kasuwar mai suna Salim, ya ce suna fatan Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba tare da fatan Allah ya mayar musu da alkhairin abin da suka yi asara.

''Munyi asarar dukiya da yawa, amma muna godewa Allah da ya takaita gobarar babu asarar rai, kuma bata murkushe kasuwar gaba daya ba''.
''Muna fatan mu da muka yi asarar dukiya, Allah ya mayar mana da alkhairi, Allah kuma ya kiyaye faruwar haka nan gaba.''

Gobara ta tashi a 'Monday Market' a Borno

A wani rahoton kun ji cewa gobara ta tashi a babban kasuwa ta 'Monday Market' da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Gobarar ta kone shaguna da dama kuma an yi asarar dukiyoyi na miliyoyin naira kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali, Zaman Makoki Yayin Da Mata Da Miji Da Yaransu 6 Suka Rasu A Gobara A Zaria

Asali: Legit.ng

Online view pixel