Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

  • EFCC mai yaki da rashin gaskiya za ta fara farautar wadanda za su bar mulki a watan Mayu
  • Abdulrasheed Bawa ya nuna an gama shirye-shiryen da suka dace wajen shari’a da masu barin gado
  • Shugaban Hukumar EFCC bai jin tsoron kiraye-kirayen da ake yi na tunbuke shi daga kan mulki

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya, ta kammala duk shirye-shirye na ram da Gwamnonin masu barin gado a kasar nan.

Da Daily Trust ta zanta da Abdulrasheed Bawa a ofishinsa da ke Hedikwatar EFCC, ya shaida mata cewa za su fara kame bayan 29 ga watan Mayun nan.

Nan da ranar 29 ga watan Mayun 2023, gwamnoni da dama za su bar ofis a sakamakon cikar wa’adi ko shan kashi a zaben tazarce da suka shiga.

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

A zantawar da aka yi da Abdulrasheed Bawa, bai fadi sunan wani Gwamna ko jami’i da za a kama ba, amma ya ce zamansu a ofis ya hana ayi ram da su.

Badakala a ma'aikatun tarayya

Dokar kasa da tsarin mulki ba su bada damar ayi shari’a da Gwamna ko Shugaban kasa mai ci ba, a dalilin haka dole a jira zuwa lokacin da su bar karaga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Baya ga shirin kama masu barin-gado, Bawa ya ce akwai wasu ma’aikatun tarayya biyu da ake bincike a kan zargin facaka da kudi wajen sayayyen kaya.

EFCC.
EFCC a Najeriya Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Shugaban na EFCC ya ce akwai ma’aikatar da ake zargin an yi amfani da kwangiloli 20, an saci N4bn ta hanyar hada kai da ma’aikata da buga takardun boge.

Ko gezau

Da yake amsa tambaya a game a kungiyoyi masu zaman kan su da ke neman a tunbuke shi, an rahoto Bawa yana mai cewa bai jin tsoron abin da ake yi.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

Matashin yake cewa shi ne shugaban EFCC na farko a tarihi da ya je kotu ya bada shaida, ya ce wasu ne suke biyan kungiyoyin nan domin a taso shi a gaba.

Bawa wanda ya ce bai jin tsoron komai, ya ce EFCC ta rasa shari’a 41, amma tayi nasara a 3, 785, ya ce ana zanga-zanga ne saboda a canza shi ganin yana aiki.

Da yardar Ubangiji daga Mayu zuwa Yuni, Bawa ya ce jami’an EFCC za ta cafke manyan mutane kuma za a fara gurfanar da wadannan mutane a kotu.

Wadanda za su bar ofis bayan watan Mayu, hukumar ta nuna a shirye ta ke da ta kamo su.

Keyamo ya rubuta takarda ga DSS

A takardar da Festus Keyamo SAN ya aikawa Darektan hukumar DSS, an ji labari Ministan ya bukaci a cafke ‘Yan takaran LP a zaben shugaban kasa.

Keyamo ya ce Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed su na kiran a rusa damukaradiyya, sun dage a bi hanyoyin da doka ba ta san da su ba.

Kara karanta wannan

Abba Gida-gida: Sabon gwamnan Kano ya yi magana, ya fadi abin da ya shiryawa Kanawa

https://dailytrust.com/efcc-to-go-after-corrupt-govs-others-after-may-29/

Asali: Legit.ng

Online view pixel