“Akwai Mai Kalubalantarta?” Amarya Ta Fita Filin Taro, Ta Girgije Cikin Salo a Bidiyo

“Akwai Mai Kalubalantarta?” Amarya Ta Fita Filin Taro, Ta Girgije Cikin Salo a Bidiyo

  • Wani dan gajeren bidiyo ya nuno amarya tana rawa da kayatar da jama'a a yayin bikin aurenta
  • Ta sanya hadaddiyar doguwar riga irin ta amare a bidiyon sannan ta dungi rawa cikin salo tana karkada kugunta
  • Masu ma'abota son rawa sun yi martani ga dan gajeren bidiyon a yanayi mai ban dariya, amma wasu da yawa sun jinjinawa amaryar

Wata amarya ta shahara a dandalin TikTok bayan ta wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda take girgijewa a wajen bikin aurenta.

Bidiyon wanda @queensillat2 ta wallafa ya nino lokacin da matashiyar ta isa filin taro sannan ta janye hankalin mutane da salon rawanta.

Amarya tana taka rawa a wajen bikinta
“Akwai Mai Kalubalantarta?” Amarya Ta Fita Filin Taro, Ta Girgije Cikin Salo a Bidiyo Hoto: @queensillat2.
Asali: TikTok

A lokacin da ta isa filin rawan, hatta ga yara sai da suka taru don kallon yanayin irin takun da take yi.

Kyakkyawar amarya sanye da doguwar riga tana girgijewa

Sanye da dinkin doguwar riga mai kyau, matashiyar ta yi rawa da dukka karfinta, tana mai jefa kafa kamar wacce za ta sauka daga dogon takalmin da ke kafarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tana ta kada hannu yayin da take girgiza kwankwasonta daidai da sautin kidan da ke tashi a sama.

Bidiyon bai fi tsawon sakanni biyar ba amma ya nuna lallai ita din gwanar iya rawa ce.

Bidiyon ya haifar da martani sosai a tsakanin ma'abota son rawa saboda yadda take takawa, wani mai amfani da TikTok ya yi ba'a cewa da ace shine angon da ya fasa auren.

Kabbi bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Nasara ta ce:

"Ina ganin suna fada mata cewa rawan ya isa hakan nan....Anti dan Allah ki kyale amarya ta ji dadin ranarta."

@aemyyyya yi ba'a:

"Da ace nine angon da na fasa auren."

@Imam amb ya yi martani:

"Ya yi kyau sosai yar'uwa."

@user6952010607612 ya yi martani:

"Kin yi matukar kyau."

@user7637097622850 ta ce:

"Kannen mijin suna kishi."'

@Esther Ghunney ta yi martani:'

"Ina ganin suna shirin kai ta gidan mijinta ne."

@Barikisu Mohammed 94 ta tambaya:

"Akwai mai kalubalantarta?"

Amarya ta yi amfani da bakinta wajen daura girki

A wani labari na daban, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wata amarya da ke daura girki da taimakon bakinta a wajen shagalin bikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel