Ango Ya ‘Dare Saman Tsani Don Tsawonsa Ya Kai Kuncin Amaryarsa a Bidiyo

Ango Ya ‘Dare Saman Tsani Don Tsawonsa Ya Kai Kuncin Amaryarsa a Bidiyo

  • Wata yar dirama ta afku a yayin wani bikin aure lokacin da angon ya hau saman tsani don sumbatar amaryarsa bayan an daura masu aure
  • Mutumin ba gajere bane chan, amma dai matar ta fi shi tsawo sosai hakan ya sa aka kawo tsanin
  • Surukinsa ne ya haifar da abun ban dariyar domin dai shine ya hawo da tsanin kan mumbarin

Wani bidiyon ban dariya a TikTok ya nuno lokacin da wani mutum ya hau saman tsani don ya sumbaci matarsa a wajen daurin aurensu.

A bidiyon wanda @swagmotive ya wallafa, an kawo tsanin ne domin mutumin ya samu damar isa ga matarsa sannan ya sumbaceta da kyau.

Ango da amarya cikin shauki
Ango Ya ‘Dare Saman Tsani Don Tsawonsa Ya Kai Kuncin Amaryarsa a Bidiyo Hoto: @swagmotive.
Asali: TikTok

A zahirin gaskiya ba wai mutumin na da gajarta sosai bane illa dai matarsa ta fi shi tsawo sosai.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohuwa ta rude, ta kone danta, matarsa da jikokinta a wata jiha

Bidiyo ya nuno ango tsaye kan tsani a gaban amaryarsa

Da ace bai hau tsanin ba, zai iya sumbatar amaryar tasa. Surukinsa ne ya haddasa yar diramar mai ban dariya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana gama ayyana mutumin da amaryar tasa a matsayin mata da miji, sai surukinsa ya gaggauta hawa mumbari da dan karamin tsanin a hannunsa.

Gaba daya wajen ya kaure da dariyar jama'a da ke cike da farin ciki yayin da mutumin mai tsananin biyayya ya haye saman tsanin kuma nan take tsawonsa ya karu sannan uya sumbaci matar tasa.

Bidiyon ya yadu sannan ya ja hankalin mutum fiye da miliyan 5 da suka kalle shi a TikTok yayin da mutane suka bayyana iyalin a matsayin masu farin ciki.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@April Sanchez ta ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

"Sai da mahaifinta ya yi masa ba'a, alaka mafi kyau."

@Rubia ta ce:

"Babu abun da ya samu gajeren sarki...Kalli yadda kowa ke farin ciki."

@user2117535827180 ya ce:

"Mahaifin na matukar farin cikin samunsa a matsayin surukinsa...kyawawan ma'aurata masu farin ciki."

Bidiyon aure da aka yi a saukake ya haddasa cece-kuce

A wani labari na daban, jama'a sun jinjinawa wasu sabbin ma'aurata kan yadda suka shirya bikinsu a saukake babu karya da son burgewa.

Kamar yadda aka gani a wani bidiyo da ya yadu, an gudanar da shagalin bikin ne a tsakar wani gida da yan uwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel