Amarya Ta Yi Amfani Da Bakinta Wajen Daga Tukunya Da Daura Shi a Wuta Yayin Bikin Aurenta a Bidiyo

Amarya Ta Yi Amfani Da Bakinta Wajen Daga Tukunya Da Daura Shi a Wuta Yayin Bikin Aurenta a Bidiyo

Wani bidiyo da ke nuna abun da ya yi kama da al'adar aure ya yadu kuma ya haifar da martani sosai a TikTok

  • A bidiyon, an gano amarya tana amfani da bakinta wajen daga karamin tukunya sannan ta daura shi a kan murhu
  • Ta kuma yi amfani da bakinta wajen diban ruwa sannan ta zuba a cikin tukunyar kamar dai tana son yin girka abinci kafin daurin auren

Wata amarya ta yadu a soshiyal midiya bayan an gano ta a wani bidiyon TikTok tana yin wani abu mai kama da al'adar aure.

A bidiyon mai tsawon minti 2 da sakan 12 wanda @debbyzimba ya wallafa, an gano amaryar da wasu mata duke a kan gwiwowinsu.

Amarya na daura girki da baki
Amarya Ta Yi Amfani Da Bakinta Wajen Daga Tukunya Da Daura Shi a Wuta Yayin Bikin Aurenta a Bidiyo Hoto: @debbyzimba.
Asali: TikTok

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Daidai Ruwa Daidai Tsaki: Bidiyon Wani Aure Da Aka Yi Shi Cikin Sauki a Tsakar Gida Ya Haddasa Cece-Kuce

Sun duka a gaban wani wutan murhu da aka hada. Matar farko ta kwatancen yadda za a daga kaamin tukunyar ta hanyar amfani da bakinta.

Bidiyon amarya tana daga tukunya da bakinta ya yadu

Da take bin misalin da aka yi, amaryar ta dauki tukunyar da babu komai a ciki da bakinta sannan ta daura shi a kan murhu.

Sai kuma ta yi amfani da bakin nata wajen rike kofi wanda ta debi ruwa da shi sai ta zuba a cikin tukunyar.

Alamu sun nuna abun da amaryar ta yi yana daga cikin al'adun aure ko yana nuna yadda za ta dunga girkawa iyalinta abinci a matsayin mace ta gargajiya. Sai dai har yanzu ba a san inda aka dauki bidiyon ba.

Tuni bidiyon ya yadu a TikTok da martani fiye da 3000 daga mutane wadanda suke da abun tofa dangane da lamarin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

Ya auri yarinya? Bincike ya gano bayanan amarya da angonta baba dattijo

@brendafrancis577sugar ta ce:

"Dan Allah ina ne nan don kada na je na fada tarkon soyayya ta wannan bangaren."

@princessfeargod1 ta yi martani:

"Allah ya kyauta! al'adun wasu mutane na bani mamaki."

@lady affluent ta ce:

"Toh idan gashin dokin ya kama da wuta fa?"

@Vickywine Heartbta tambaya:

"Wato hakan na nufin idan ba ki da lafiya ba za ki iya amfani da hannu wajen girki ba kenan, dole ka girkawa iyalinki abin ci a haka."

@user7782207026467 ta ce:

"Kai mutanena na 256 ku zo ku ga shagalin bikin aure."

Bidiyon wasu ma'aurata da suka yi bikinsu a tsakar gidansu ya yadu

A wani labarin kuma, bidiyon wasu sabbin ma'aurata da suka yi aurensu cikin sauki a tsakar gidansu ya yadu a TikTok kuma mutane da dama sun jinjina masu kan yadda suka yi abun su a saukake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel