Zababben Gwamnan Sokoto Aliyu ya bayyana Manufofi 9 da Yake Son cimmawa A Mulkinsa

Zababben Gwamnan Sokoto Aliyu ya bayyana Manufofi 9 da Yake Son cimmawa A Mulkinsa

  • Zababben gwamnan jihar Sokoto ya bayyana kudurin cika alkawuran da ya daukarwa ‘yan jihar a kamfen da ya yi
  • Alhaji Ahmad Aliyu ya ce, zai yi musu wasu abubuwa tara da ya tsara a cikin mulkinsa na shekaru hudu
  • Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben jihohi a Najeriya, har yanzu akwai wadanda ba a sanar da nasu ba

Jihar Sokoto - Alhaji Ahmad Aliyu, zababben gwamnan jihar Sokoto ya bayyana manufofi 9 na gwamnatinsa, da kuma hanyoyin da zai bi don ciyar da jihar gaba.

Ya bayyana wadannan manufofi ne a lokacin da yake yin taron manema labarai na farko a ranar Litinin a jihar ta Sokoto, PM News Nigeria ta ruwaito.

Da yake bayyana manyan matsalolin da yake son magancewa, Aliyu ya yi alkarin inganta fannin ilimi, harkar lafiya da kuma samar da ruwan sha.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Mutum 3 Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsari Da Ya Cika da Ayarin Gwamnan Katsina

Zababben gwamnan Sokoto ya yi alkawari 9
Zababben gwamnan Sokoto, Alhaji Ahmad Aliyu | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Abubuwan da ya tsara yiwa jama'ar Sokoto

Sauran abubuwan da yace zai maida hankali a kansu sun hada da noma, tsaro, karfafa matasa, inganta harkar kananan hukumomi, addinai da tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, cewa ya yi:

“Gwamnatina za ta saurari koke da burin ‘yan jihar bisa hangen hanyar cimma alkawuran kamfen.
“Zan karfafa aikin gwamnati ta hanyar yin gyara mai kyau, sannan na tabbatar da ana biyan albashi, fanso da giratuti a kan kari. Gwamnati na za ta saurari suka da gyara daga dukkan ‘yan Najeriya.”

Yadda zaben gwamnan jihar ya kasance

A zaben ranar Asabar da ta gabata, Aliyu dan APC ya samu kuri’u 453,661, inda ya doke abokin hamayyarsa na PDP, Malam Sa’idu Umar mai kuri’u 404,632.

Aliyu ya yabawa hukumar zabe bisa jajircewa wurin tabbatar zabe na gaskiya a matakin gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a kasar nan, Gazette ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Dan takaran Sanatan APC a Kaduna Zai Tafi Kotu, Ya Fito da Hujjojin Magudin PDP

A cewarsa, nasararsa na nufin an zabe shi domin ya yi iyakar kokarinsa wajen ciyar da jihar Sokoto gaba.

Ya mika godiya ga jiga-jigan APC

A bangare guda, ya bukaci abokan hamayyarsa da su yi hakuri, su daddara su dauki faduwarsu a matsayin kaddara kana su dafa masa don yiwa jihar hidima.

Ya bayyana godiyarsa ta musamman ga Sanata Aliyu Wamakko, ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, shugaban APC na jihar, Alhaji Sadiq Achida da sauran manya da kananan magoya bayan APC.

A jihar Yobe, an sanar Mai Mala Buni na APC a matsayin wanda ya sake lashe zaben gwamna a karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel