Yanzu Yanzu: Abun Bakin Ciki Yayin da Mutum 3 Suka Mutu a Hatsarin Mota Da Ya Cika Da Ayarin Gwamnan Katsina

Yanzu Yanzu: Abun Bakin Ciki Yayin da Mutum 3 Suka Mutu a Hatsarin Mota Da Ya Cika Da Ayarin Gwamnan Katsina

  • Rayuka uku sun salwanta yayin da mummunan hatsarin mota ya cika da ayarin Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina
  • Mutane uku da suka hada da jami'an tsaro biyu da dan farin hula daya sun kwanta dama a ayarin gwamnan Katsina a ranar Juma'a
  • Suna a hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Kafur inda gwamnan zai kada kuri'a a zaben gwamna a mahaifarsa lokacin da suka yi hatsarin

Katsina - Akalla mutum uku ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya cika da ayarin Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mummunan hatsarin ya afku ne yayin da gwamnan ke a hanyarsa ta zuwa mahaifarsa da ke Masari a karamar hukumar Kafur ta jihar a daren ranar Juma'a, 17 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

An Rasa Rayyuka 17 A Mummunan Hadarin Mota A Jihar Kano

Gwamna Aminu Masari yana jawabi
Yanzu Yanzu: Abun Bakin Ciki Yayin da Mutum 3 Suka Mutu a Hatsarin Mota Da Ya Cika Da Ayarin Gwamnan Katsina Hoto: Aminu Bello Masari
Asali: Facebook

Abun da ya wakana

An tattaro cewa yana hanyar zuwa mahaifar tasa ne domin yin zaben gwamna da na majalisar jiha da za a yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris lokacin da lamarin ya afku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyoyi sun ce jami'an yan sanda biyu da wani dan farin hula daya ne suka rasa ransu a hatsarin, rahoton Solace Base.

Zaben gwamnoni: Yadda limamin masallaci ya yi tofin Allah tsine ga masu shirin magudi, Shehu Sani

A wani labari na daban, tsohon dan majalisa da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya bayyana cewa wani limami ya yi tofin Allah tsine ga wadanda ke shirin yin magudi a zaben gwamnoni.

Shehu Sani ya ce ga mamakinsa, sai ya ga wasu mutane da ke wajen sun ki amsa addu'an da 'Amin' yayin da limamin ya nemi fushin Allah ya kasance kan duk wanda ke shirin murdiya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kashe Mutum 4 Yayin Arangama Tsakanin Yan Shi'a Da Tawagar El-Rufai A Kaduna

Jihohin Najeriya dai za su zabi sabbin gwamnonin da za su shugabance su na wasu shekaru hudu masu zuwa a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

A wani labarin kuma, rundunar yan sanda ta sha alwashin bi ta kan duk wasu miyagu da za su kawo tsaiko ga gudanarwar zaben da za a yi a yau Asabar.

Yan sandan sun jaddada shirinsu na bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyin jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel