Sakamakon Zaɓen Gwamnoni Na 2023: Jerin Zaɓaɓbun Gwamnoni 5 Da Suka Ci Zaɓe Da Ƙuri'u Mafi Ƙaranci

Sakamakon Zaɓen Gwamnoni Na 2023: Jerin Zaɓaɓbun Gwamnoni 5 Da Suka Ci Zaɓe Da Ƙuri'u Mafi Ƙaranci

  • Zaben 18 ga watan Maris na gwamnoni da yan majalisun jiha ya kasance daya daga cikin mafi tarihi a siyasar Najeriya
  • Bayan sanar da sakamakon zaben gwamnoni, jam'iyyar APC ta fadi a wasu jihohi, jam'iyyar PDP ta farfado da karsashinta, yayin da jam'iyya mai tasowa LP ta kafa tarihi
  • Sai dai, duk da yadda aka gudanar da zaben, akwai jihohin da aka samu karancin ma su kada kuri'a an kuma tattara guda 5

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da wanda su ka lashe zaben gwamnoni na 18 ga watan Maris a jihohi 26 tare da bayyana jihohin Adamawa da Kebbi a matsayin idan zabe bai kammala ba.

Sai dai, an bayyana wasu daga cikin wanda su ka lashe zaben gwamnan a jihohinsu da mafi kankantar kuri'u. Hakan ya faru sakamakon karancin fitowar ma su kada kuri'a a jihohin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Jigon PDP ya janye daga takara a zaben fidda gwamin gwamna a wata jiha

Zababbun gwamnoni
Sunayen zababbun gwamnoni wadanda suka ci zabe da kuri'u mafi karanci. Hoto: Photo Credit: Ogbu Kefas
Asali: Twitter

Ga jerin guda biyar a kasa:

1. Peter Mbah, Enugu

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan Jihar Enugu, shi aka bayyana a matsayin wanda ya yi nasara da kuri'u 160,895 in da ya kayar da babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar LP, Chijioke Edeoga, wanda ya samu kuri'a 157,552.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tazarar kuri'a tsakanin wanda ya yi nasara da na biyunsa 3,343 ce. Bisa kididdiga, jihar ita ce mafi karancin wanda su ka fito kada kuri'a.

2. Alex Otti, Abia

INEC ta bayyana Alex Otti, na jam'iyyar Labour a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Jihar Abia, bayan samun kuri'u 175,466.

Otti ya kayar da dan takarar PDP, Okechukwu Ahiwe, wanda ya samu kuri'a 88,526 a zaben. Abia ita ce jiha ta biyu da ba fita zabe sosai ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

3. Francis Nwifuru, Ebonyi

Ebonyi na daya daga cikin jihohin da ba a samu masu yawan kada kuri'a ba, in da dan takarar APC, Francis Nwifuru ya lashe zaben da kuri'a 199,131.

Nwifuru ya kayar da dan takarar jam'iyyar APGA a zaben da aka gudanar kusan kankankan.

4. Agbu Kefas (Ritaya), Taraba

A cikin jerin jihohin akwai Jihar Taraba, in da Agbus Kefas na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a 257,926 wanda ya kayar da Muhammad Yahaya na jam'iyyar NNPP, mai kuri'u 202,277.

Wanda ya zo na uku a zaben Emmanuel Bwacha, dan takarar APC ya samu kuri'a 142,502.

5. Bassey Otu, Cross River

Bassey Otu, dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan na 18 ga watan Maris a Jihar Cross River, ya lashe zaben zaben da kuri'a 258,619 fiye da dan takarar PDP, Sandy Onor, wanda ya samu kuri'a 179,636.

Kara karanta wannan

"INEC Ta Yi Kuskuren Ayyana Abba Gida-Gida Matsayin Zababben Gwamnan Kano", Masu Sa Ido Kan Zabe

Cross River na daya daga cikin jihohin da ke samar da man fetur a Najeriya amma duk da haka an samu karancin ma su kada kuri'a a zaben gwamnan da yan majalisar jiha.

Festus Keyamo Ya Fada Tinubu Abin Da Ya Kamata Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi

A wani rahoton, Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da samar da ayyuka kuma mai magana da yawun kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, ya bayyana abin da mai gidansa, zababben shugaban kasa Bola Tinubu zai fara yi da zarar an rantsar da shi a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel