EFCC Ta Tura Jami’anta 150 Zuwa Jihohin Kano, Katsina da Jigawa a Shirin Zaben Gwamnoni

EFCC Ta Tura Jami’anta 150 Zuwa Jihohin Kano, Katsina da Jigawa a Shirin Zaben Gwamnoni

  • Kwamandan EFCC a jihar Kano ya bayyana yadda hukumar ta dauki jami’anta ta kai jihohin Kano, Katsina da Jigawa
  • Hukumar ta ce, za ta tabbatar da an yi zabe lafiya, kuma nagartacce a lokacin da ake ci gaba da fuskantar dar-adar
  • An daga zaben gwamnoni a Najeriya daga ranar 11 ga watan Maris zuwa 18 ga watan Maris saboda dalilai

Jihar Kano - Gabanin zaben ranar Asabar mai zuwa na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tura jami’anta 200 dauke da makamai zuwa jihohin Kano, Katsina da Jigawa.

Rahoton da muke samu daga jaridar Punch ya bayyana cewa, jami’an za su yi aiki ne don tabbatar da ba a yi cinikiyyar kuri’u ba a zaben da za a yi.

Kwamandan shiyya na jihar Kano a EFCC, Mr. Farouk Dogondaji ne ya bayyana shirin hukumar a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnoni: Jihohi 28 ne za a yi zabe gobe Asabar, ga jerin sunayensu

An tura jami'an EFCC Kano, Jigawa da Katsna
Hukumar EFCC mai yaki da rashawa a Najeriya | Hoto: punchng.cpm
Asali: UGC

Dalilin tura jami’ai a jihohin

Dogondaji ya bayyana cewa, tura jami’an na daya daga cikin aikin hukumar don tabbatar da an yi zabe cikin tsanaki kuma na gaskiya a shiyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Mun tura jami’ai 50 don sanya ido a zaben jihar Kano, 50 a cikin Jigawa da kuma 50 a cikin jihar Katsina don hana siyan kuri’u kwata-kwata a lokacin zaben.”

Ya kuma bayyana cewa, sauran jami’an an tura su ne zuwa filin jirgin Aminu Kano da kuma na Umar Musa Yar’adua da ke Katsina.

Yadda EFCC tatsara aikin zabe a shiyya

Ya kara da cewa:

“Za mu bayyana a fili a mazabun sanata guda tara na jihar Kano, Katsina da jihohi don sanya ido cikin tsanaki kan aikin zaben gaba dayansa.
“Za kuma mu bayyana a cibiyoyin tattara sakamakon zabe don dakile lalata sakamakon zabe daga kananan hukumomi har matakin jiha.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: DSS Ta Kama Yan NNPP 2 Da Ke Shirin Tada Zaune Tsaye Yayin Zaben Gwamna a Kano

“Za mu sanya ido ne kan aikin gaba dayansa tare da hukumar tsaro ta farin kaya don tabbatar da an yi zabe lafiya kuma ‘yan kasa da suka cancanta sun zabi shugabannin da suke so a karkashin kulawarmu.”

EFCC za ta taimaka a yi zaben gaskiya

Dogondaji ya yi amanna da cewa, halartar jami’an EFCC a wuraren zaben zai taimaka matuka wajen gudanar da zabe na gari a kasar.

Daga karshe, ya yi kira ga iyaya da kada su bari ‘ya’yansu su shiga harkar dabanci domin kuwa za a kama su kuma a tabbatar da an hukunta su.

A baya an dage zabe a Najeriya saboda rikicin da ka iya faruwa da kuma rashin cikakken shirin hukumar zabe mai zaman kanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel