Gwamnatin Okowa Ta Roki Mutanen Delta Su Ci Gaba da Karban Tsohon Kuɗi

Gwamnatin Okowa Ta Roki Mutanen Delta Su Ci Gaba da Karban Tsohon Kuɗi

  • Gwamnatin jihar Delta karkashin abokin takarar Atiku ta roki 'yan jihar su bi umarnin babban banki CBN
  • Kwamishinan yaɗa labarai ya ce gwamnatin ba ta da masaniyar wahalar da mutane suka sha sanadin sauya naira
  • Ya roki yan kasuwa, gidajen mai, masu karban harajin gwamnati da sauransu su karbi tsohon naira

Delta - Gwamnatin jihar Delta karkashin jagorancin gwamna Ifeanyi Okowa ta roki mazauna jihar su yi biyayya ga umarnin babban bankin Najeriya (CBN).

Punch ta tattaro cewa CBN ya umarci 'yan Najeriya su ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200, N500 da N1000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Takardun tsohon naira.
Takardun tsoffi naira N1000 Hoto: vanguard
Asali: Depositphotos

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Delta, Mista Charles Aniagwu ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya fitar a Asaba, babban birnin jiha.

Kara karanta wannan

Bayan Maganar Buhari, CBN Ya Tsawaita Wa'adin Amfani da Tsoffin Naira N500 da N1000

Ya roki mazauna jihar da su ci gaba da harkokin gabansu da tsoffin takardun kuɗin duba da hukuncin Kotun koli da CBN, wanda ya tsawaita halascin amfani da takardun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan ya yi kira ga ma'aikatan da ke tattara harajin gwamnati, gidajen mai, masu Tireda, 'yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki su bi umarnin CBN.

Bamu san mutane sun shiga wahala ba - Gwamnatin Delta

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Delta ba ta san sabon tsarin sauya fasalin naira ya jefa mutane cikin ƙaƙanikayi da wahalhalun rayuwa ba.

Amma duk da haka, Mista Aniagwu ya bukaci mazauna su yi amfani da wannan damar da hukuncim Kotun koli ya samar musu, su rage raɗaɗi da kuncin da tsarin ya haifar masu.

Vanguard ta ce daga nan ya yi kira ga dukkan hukumomin gwamnatin Dele masu alhaki da sauran masu ruwa da tsaki da su karbi tsohon kuɗi daga hannun mutane.

Kara karanta wannan

Gwamna APC Ya Faɗi Muhimmiyar Maganar da Ya Yi da Gwamnan CBN Kan Sauya Naira

"Muna shawartan hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki, kar su ki karban tsohon kuɗi idan mutane sun yi amfani da su wajen biyan wani haƙƙi."

Ku Bi Umarnin Kotun Koli Kan Tsohon Naira - Buhari

A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa CBN umarni kan amfani da tsohon N500 da N1000.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, Mallam Garba Shehu, ya ce babu dalilin da CBN zai fake da jiran umarnin Buhari gabanin bin umarnin Kotu.

Wannam na zuwa a daidai lokacin da ake sukar gwamnatin shugaba Buhari kan yin kunnen uwar shegu da hukuncin Kotu mai daraja ta farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel