An yi Ba Ayi Ba: Har Yanzu Bankin CBN Ya Ki Fito da Tsofaffin N500 da N1000 a Najeriya

An yi Ba Ayi Ba: Har Yanzu Bankin CBN Ya Ki Fito da Tsofaffin N500 da N1000 a Najeriya

  • Babban bankin CBN ya yi biyayya ga umarnin kotu na halatta cigaba da kashe N500 da N1000
  • Amma duk da hakan, bankuna da-dama sun tabbatar da cewa CBN bai fito da tsofaffin kudin ba
  • Har yanzu ana shan wahala wajen samun tsabar kudi, da wahala a iya ba ka N20000 a tashi daya

Abuja - Maganar da ake yi har zuwa yanzu, babban bankin CBN bai fito da tsofaffin N500 da N1000 da ya karbe daga hannun jama’a a Najeriya ba.

Wani bincike da Daily Trust ta gudanar ya shaida mana cewa duk da bankin na CBN ya yi biyayya ga umarnin kotu, ba a fito da kudin da ke ajiye ba.

A halin yanzu mutane su na cigaba da shan matukar wahalar samun kudi daga bankunansu.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: Bankuna sun fara ba da tsoffin Naira, amma sun gindaya sharadi mai tsauri

‘Yan kasuwa, masu sana’ar hannu, dalibai da masu kasuwancin POS sun shaida cewa da suka je bankunansu, ba su samu adadin da suke nema ba.

Sai dai a samu N5000 ko N10000

Wasu sun fadawa manema labarai cewa N5000 zuwa N10000 kadai suka iya samu a bankuna, wasu kuma sun taki sa'a, an ba su abin da ya kai N20, 000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani babban ma’aikacin bankin Guarantee Trust Bank ya ce CBN bai ba su tsofaffin kudi, don haka sai dai su ke rabawa mutanensu abin da suka adana.

'yar kasuwa
Wata 'yar kasuwa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wata majiya ta ce bankuna sun boye tsofaffin kudin da suka karba kafin wa’din 10 ga watan Fubrairu, daga baya sai kotu ta halatta kashe N500 da N1000.

Akwai wani ma’aikacin banki da ya fadawa Daily Trust ba su karbi tsofaffin kudi daga hannun CBN ba, amma ya ce dalili shi ne ba su karar da na su ba.

Kara karanta wannan

Rikicin Naira: Masu gidajen mai sun ki karbar tsoffin kudi duk da umarnin CBN, sun fadi dalili

Ana nan a gidan jiya

Da Legit.ng Hausa ta tattauna da wani a bankin Jaiz a garin Abuja, ya ce kudin da suka karba a lokacin da CBN ta bada damar maida kudi suke fito da su.

Wannan ma’aikaci ya ce a lokacin ba su tattara kudin sun maidawa babban banki ba, sannan ya ce har yau ba a bada fiye da N20, 000 domin dokar ta na aiki.

Da sababbin kudin da tsofaffin duka sun yi wahala, haka wani mai aiki da Union Bank ya shaida mana dazu, ya ce iyakarta a iya ba mutum N10, 000.

A dakatar da Emefiele

A ranar Laraba aka samu rahoto cewa Darektan yada labarai na kwamitin takarar Bola Tinubu ya na so a sauke Godwin Emefiele daga Gwamnan CBN.

Bayo Onanuga yana ganin babu dalilin da Emefiele zai cigaba da rike CBN bayan kotu ta tilasta masa yin watsi da canjin takardun kudin da ya fito da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel