Dillalan Man Fetur Sun Ki Batun Karbar Tsoffin Takardun Naira Duk da Umarnin CBN

Dillalan Man Fetur Sun Ki Batun Karbar Tsoffin Takardun Naira Duk da Umarnin CBN

  • Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta bayyana rashin amince da kashe tsoffin kudi duk da umarnin kotu da na CBN
  • Wannan na zuwa ne a ranar Litinin, inda aka tattauna da wani shugaban kungiyar kan matsayarta a wannan karon
  • Tun bayan kawo batun sauyin Naira, an sha samun cece-kuce da sabani tsakanin ‘yan Najeriya da bankunan kasar nan

Najeriya - Dillalan man fetur a ranar Litinin sun ci gaba da bayyana rashin amincewarsu da karbar tsoffin takardun Naira daga hannun mutane, duk da cewa CBN ya ba da umarnin a ci gaba da karbar kudin.

An kuma tattaro cewa, har yanzu bankuna basu yi magana da dillalan mai da masu gidajen mai ba game da ci gaba da karbar tsoffin kudin a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

“Kudi Da Nake Nema” Matashi Ya Yi Bidiyon Buhuhunan Tsoffin Kudi Da CBN Ya Nika Ya Watsar

Dillalan na mai sun bayyana cewa, ya kamata tunda gwamnati ta dauki kudurin sauyin kudi, to kawai ta kaddamar da abin da take so ta daina sanya ‘yan Najeriya a cikin rudani.

Rudani kan sabbin kudi da tsoffi bayan umarnin CBN
Yadda sabbin kudi da tsoffi ke ci gaba da jawo rudani a Najeriya | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Sakataren kungiyar dillalan ta IPMAN a Abuja-Suleja, Muhammad Shugaibu ya bayyana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Sun ce sun sauya fasalin kudi, tunda haka ne babban bankin kasa sai ya fitar da sabbin kudin. Meye yasa suke mayar damu baya suna rudar da mutane? Meye za mu yi da tsoffin kudin?”

Sai bankuna sun fara karbar tsoffin kudi kafin mu karba

Hakazalika, ya bayyana damuwa game da yadda CBN ya bayyana lalata tsoffin kudaden, inda yace a yanzu yana da wahala ma a samu tsoffin kudin a hannun jama’a.

Ya shaidawa Punch cewa:

“Sai bankuna sun fara karba kafin mu fara daga hannun jama’a. Amma dai a iya fahimtarmu, ba za mu karbi tsoffin kudi a ko daya daga gidajen man mu ba.”

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Masani ya fadi kura-kurai 5 da CBN ya yi wajen kawo batun sauyin Naira

Ya kuma bayyana cewa, a halin da ake ciki, gidajen mai a kasar na amfani da POS ne wajen siyar da mai ko kuma ta hanyar amfani da sabbin kudi.

Akwai rudani a lamarin

Shuaibu ya kuma bayyana shakku game da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa CBN ya lalata tsoffin N500 da N1000 da aka mayar bankuna.

Daga karshe, ya bayyana rudanin da ke tattare da umarnin kotun kolin kansa na ci gaba da kashe tsoffi da sabbin kudin a tare.

A wani bidiyo, an ga wasu tarin kudaden da aka lalata su a Najeriya bayan umarnin shugaban kasa na lalata tsoffin Naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel