Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Amaryarsa Suka Ta Da Kura a Soshiyal Midiya

Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Amaryarsa Suka Ta Da Kura a Soshiyal Midiya

  • Jama'a sun yi cece-kuce bayan cin karo da bidiyon wani mutum mai shekaru da ya yi wuff da wata kyakkyawar budurwa
  • An dai gano angon wanda ya cika da farin ciki yana yane lullubin da aka yi wa amaryar tasa wanda ke nuna ana budar kai ne
  • Sai dai mutane da dama suna ganin sam wannan hadin bai yi duba ga tazakarar shekaru da ke tsakaninsu

Jama'a a soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da hoto da bidiyon wasu ma'aurata sabbin aure.

Angon wanda shekaru suka dan fara ja masa ya yi wuff da wata tsaleliyar budurwa danya shakaf.

Tazarar shekaru da ke tsakanin sabbin ma'auratan shine abun da ya fi jan hankalin jama'a zuwa wurinsu inda sam wannan al'amari bai yi wa wasu dadi ba.

Ango yana bude kan kyakkyawar amaryarsa
Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Amaryarsa Suka Ta Da Kura a Soshiyal Midiya Hoto: hausaa_fulanii
Asali: Instagram

A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya kuma shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram ya nuno inda ango ke bude kan amaryarsa cike da farin ciki da zumudi.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Koka Yayin da Ta Ci Karo Da Mahaifiyarta Tana Karanta Hirarta Da Saurayinta a WhatsApp, Bidiyon Ya Yadu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da dama sun ce a ganin farko da suka yi wa hoton, sun zata uba ne da 'yarsa suke bankwana yayin da za a kaita dakin aurenta sai dai labari ya sha banban duba ga yanayin abubuwan da suka faru a bidiyon.

Ga hoto da bidiyon a kasa:

Martanin jama'a

Legit.ng Hausa ta zakulo wasu daga cikin martanonin da jama'a suka yi a kan wannan aure a kasa:

sadia_nas ta yi martani:

"Masu cewa ai aure ne, sunnah aka raya ya fi a kama ma ta hotel, ku dubi yarinyar nan ku dubi shekarun mutumin nan me yasa bai samo bazawara ba ko wata babbar mace? ko wadda Mijinta ya mutu? ku gaya ma ni a gidan Ubanwa su ka dace?? Wallahi ku ji tsoron Allah, ko a musulunci akwai inda a ke gargadi akan irin wannan auren…a ina zai iya da yarinyar nan? don dai shi namiji kullum a rayuwa shi a ke favoring? comment kuma sai mun yi, wanda ya ce a yi posting a social media ."

Kara karanta wannan

Wasa Da Rai: Bidiyon Wata Kyakkyawar Budurwa Cikin Zakuna Ya Janyo Cece-Kuce

zarah_duchess ta ce:

"AMARYA ALLAH YA BAKI IKON DAUKAR KAYA."

_zainiiiii ta yi martani:

"Tsakani da Allah wanan ba daidai bane bata yi kama da tana farin ciki ba mtswwww."

walinsky9 ya ce:

"Yafi Wanda suke kai kamarta hotel. Ayi ahankali don sunnah ya raya kar a kauce layi."

aishashaheeda ta ce:

"Ko kunya babu. Tsoho kato dakai, kaje ka auro yarinyar da bata wuce yar cikinka ba. Kayan bacin rai."

la_eeeshars_kitchen ta rubuta:

"Allah mun gode maka da ka bamu iyaye na gari masu hangen nesa."

Yadda uwa ta karance hirar budurwar diyarta da saurayinta a waya

A wani labari na daban, mun ji cewa wata budurwa ta shiga tsananin tashin hankali bayan cin karo da mahaifiyarta tana karanta hirarta da saurayinta a wayar tarho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel