Sannu Da Kokari: Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Cikin Zakuna Ya Dauki Hankula

Sannu Da Kokari: Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Cikin Zakuna Ya Dauki Hankula

  • Wata kyakkyawar budurwa ta ba mutane mamaki a yanar gizo bayan ta sanya bidiyonta tare da wasu zakuna biyu suna tafiya a gabanta
  • Budurwar bata nuna wani tsoro ba a gaban zakunan yayin da suke tafiya kamar wasu abokai
  • Masu amfani da soshiyal midiya waɗanda suka kalli bidiyon nata sun yi mamakin yadda ta jure ta tsaya kusa da zakunan ba tare da jin wani tsoro ba

Wata matashiyar budurwa mai amfani da sunan (@tshxlo_felo_) a TikTok, ta sanya wani bidiyo inda ta nuna lokacin da take tafiya a tsakanin wasu manyan-manyan zakuna ba tare da jin tsoro ba.

Budurwar tana sanye da ɗan guntun wando da baƙar riga, ta cigaba da tafiya cikin ƙasaita a bayan zakunan kamar wasu abun wasanta.

Zakuna
Sannu Da Kokari: Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Cikin Zakuna Ya Dauki Hankula Hoto: TikTok/@tshxlo_felo
Asali: TikTok

Zakunan suna jujjuyawa a bayan ta kamar wasu masu yi mata rakiya. A yayin da take tafiya a bayan zakunan, tana riƙe da sanda a hannun ta.

Kara karanta wannan

"Ya Yi Wuff Da Tsaleliyar Budurwa": Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Ya Wuff Da Kyakkyawar Yarinya Ya Haddasa Cece-Kuce

Mutane da dama da suka kalli bidiyon ta, sun bayyana cewa koda wasa ba zasu taɓa yin irin wannan kasadar ba a rayuwar su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon ya yaɗu sosai

Bidiyon ya yaɗu sosai inda sama da mutum dubu biyu suka yi sharhi a kan sa yayin da sama da mutum dubu ɗari suka danna masa alamar 'like'

Ga kaɗan daga cikin waɗanda muka tattaro:

Icon ya rubuta:

"Da ina tsoron Samson saboda ya halaka zaki, amma ina tsoron wanda ya halaka Samson."

YA PLACE ya rubuta:

"Idan ban da ni wanene yayi ƙoƙarin ganin bidiyon ko ba na gaske bane?"

Touch One ya rubuta:

"Sarakuna suna kare sarauniya."

Ruthy Blossom ta rubuta: "l

"Ba zan iya abinda kika yi ba. Allah ya sanya sai na rayu har naga ƴan ƴaƴana, Amen."

Kara karanta wannan

Gwarzon Namiji: Matashi Yayi Wuff Da Mata Biyu a Tare, Sun Samu Juna Biyu a Lokaci Ɗaya, Bidiyon Ya Yaɗu

Gwarzon Maza: Matashi Ya Auri Mata Biyu a Tare, Sun Samu Juna Biyu Lokaci Daya

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya janyo cece-kuce a yanar gizo, bayan bayyanar bidiyon sa tare da matan sa guda biyu.

Matashin dai yayi wuff da kyawawan matan nasa ne a tare, sannan suka samu juna biyu a lokaci ɗaya, inda daga bisani suka haihu a.lokaci ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel