Tashin Hankali Yayin da Budurwa Ta Kama Mahaifiyarta Tana Karanta Hirarta Da Saurayinta

Tashin Hankali Yayin da Budurwa Ta Kama Mahaifiyarta Tana Karanta Hirarta Da Saurayinta

  • Wani bidiyon mai ban dariya da karya zuciya na wata uwa da ke karanta hirar diyarta a waya ya yadu
  • Matashiyar ta ci karo da mahaifiyarta a falon gidansu tana karanta hirarta da saurayinta a dandalin sadarwa
  • Matashiyar ta kadu sannan ta yi kamar tana kallon TV yayin da yayarta ta dauki bidiyon cike da fargaba

Har yanzu ana muhawara dangane da matakin yarda da kuma irin yanci da ya kamata iyaye su baiwa yaransu ta bangaren hirarrakinsu a dandalin soshiyal midiya.

Wannan ya sha banban daga shekarun yara, jinsinsu, tarbiyarsu, wayewarsu da kuma yanayin abokai da hankalin yaron.

Budurwa da mahaifiyarta tana karanta sakonninta
Tashin Hankali Yayin da Budurwa Ta Kama Mahaifiyarta Tana Karanta Hirarta Da Saurayinta Hoto: @gossipmilltv
Asali: TikTok

A cikin wani bidiyo, wata matashiya ta dauki mahaifinyarta tana karanta irin hirar da kanwarta ke yi a dandalin WhatsApp.

Mahaifiyar tasu ta mayar da hankali sosai yayin da take karanta hirar yarinyar da saurayinta.

Kara karanta wannan

Wata Mata Mai Shayarwa Ta Jefar Da Jinjirinta Yayin Tserewa Daga Yan Bindiga A Neja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar ta yi hakan ne a gaban yan matan nata guda biyu cike da karfin gwiwa.

Yarinyar da ake gudanar da bincike a kan wayarta ta mayar da hankali sosai a kan talbijin.

Babbar ita ce ta dauki bidiyon amma alamu sun nuna ta shiga halin tsoro da fargaba a kan al'amarin.

Jama'a sun yi martani

@big_moren ta rubuta:

"Ina matukar farin ciki don na wuce wannan matakin a rayuwata. Na wahala na ci duka a rayuwata ni da nake tura hotunan rabin tsaraicina ga tsohon saurayina mahaifiyata ta kusa kashe ni a wannan ranar har sai da na dawo cikin hankalina na fara goge hirar da muka yi nan take."

@sidwell ta yi martani:

"Yarinyar nan bata ganin talbijin da take kallo."

@high_chennata ce:

"Ta yi bankwana da sake mallakar waya."

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Manyan Arewa Sun Fada Wa Shugaba Buhari Abinda Zai Faru Idan Ya Ki Bin Umarnin Kotun Koli

@okikiola_micheal1 ta rubuta:

"Mahaifiyata ta yi haka ita ma...a koda yaushe tana karanta hirata a wancan lokacin...ta zo ta karanta yanzu, ba za ta san inda kanta yake ba na tsawon kwanaki arba'in...abun da take neman za ta gani."

Kalli bidiyon a kasa:

Yadda matashiya ta fallasa magidancin da ya neme ta da lalata

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta garzaya soshiyal midiya don fallasa wani magidanci da ke neman ya kwanta da ita inda ta baje kolin hirar shi da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel