NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Naira da Fetur

NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Naira da Fetur

  • Kungiyar kwadugo ta yi barazanar shiga yajin aiki idan FG ba ta magance karancin naira da Fetur ba
  • NLC ta baiwa gwamnati wa'adin kwanaki 7 ta kawo karshen matsalolin ko ma'aikata sun fara yajin aiki
  • 'Yan Najeriya na fama da wahala da kuncin rayuwa tun bayan kirkiro tsarin sauya takardun naira na CBN

Ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ranar Litinin ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 7 ta magance matsalar karancin Man Fetur da karancin naira.

Daily Trust tace shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, shi ne ya bayyana haka yayin jawabi ga 'yan jarida a Labour House game da sakamakon taron da kwamitin gudanarwa ya kira.

Joe Ajaero.
NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Naira da Fetur Hoto: punchng
Asali: UGC

Ya ce ƙungiyar zata tsunduma yajin aiki a dukkan sassan Najeriya da kuma zanga-zanga idan har FG ba ta magamce waɗannan matsalolon cikin mako ɗaya ba.

Kara karanta wannan

Gwamna APC Ya Faɗi Muhimmiyar Maganar da Ya Yi da Gwamnan CBN Kan Sauya Naira

Mista Ajaero, wanda ya nuna damuwarsa kan karuwar wahalhalu ga yan Najeriya sakamakon tsarin CBN na sauya naira, ya yi gargaɗin cewa idan wa'adin ya kare ma'aikata zasu daina fita aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan shugaban NLC ya yi Allah wadai da lamarin ƙarancin man Fetur, inda ya ƙara da bayanin cewa tuni an kai ma'aikata da sauran gama garin 'yan Najeriya bango.

Punch ta rahoto yana cewa:

"Dangane da wadan nan batutuwan na man fetur da ƙarancin takardun naira, ƙungiyar kwadugo na sanar da gwamnatin tarayya cewa ba maganar ta yi shiru da bakinta daga yanzu."
"NLC ta baiwa babban bankin Najeriya da gwamnatin tarayya wa'adin kwanakin aiki 7 su kawo karshen lamarin nan."
"Idan har ba su yi abinda ake bukata ba har kwanaki 7 nan suka kare, kowane ma'aikaci a Najeriya ya zauna a guda."

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Ku daina baiwa Mutane Tsoffin Naira Idan Ba Zaku Karba Ba, Adeleke Ga Bankuna

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Osun ya gargaɗi bankunan kasuwanci su dakatar da mummunar ɗabi'ar da suka tsiro da ita

Ademola Adeleke ya ce gwamnatinsa ba zata zuba ido tana kallo bankuna na zaluntar talakawan da ya ke mulka.

Ya bukaci daraktan CBN na jihar Osun ya gaggauta dawo da bankuna kan hanya game da amfani da tsoffin takardun naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel