Canjin Kudi: Gwamna Abiodun Ya Tattauna da Emefiele, Ya ce Sauki Na Gab da Zuwa

Canjin Kudi: Gwamna Abiodun Ya Tattauna da Emefiele, Ya ce Sauki Na Gab da Zuwa

  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana abinda ya tattauna da gwamnan CBN kan tsarin canjin kuɗi
  • Abiodun ya tabbatarwa yan Najeriya cewa labari mai daɗi na nan tafe kan amfani da tsohon naira
  • Ana ta kai kawo kan amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 tun bayan hukuncin Kotun koli

Ogun - Gwamnan jihar Ogun, ya ƙara wa yan Najeriya fata mai kyau bayan ya yi magana da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, kan wahalhalun ƙarancin naira sanadin sauya fasalin N200, N200, N500.

Gwamnan ya ce ya damu matuƙa ganin yadda 'yan Najeriya suka shiga ƙunci da wahala kowace rana sakamakon karancin takardun kuɗi a hannu da kuma rashin karban tsohon naira.

Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun.
Canjin Kudi: Gwamna Abiodun Ya Tattauna da Emefiele, Ya ce Sauki Na Gab da Zuwa Hoto: Dapo Abiodun
Asali: UGC

Da yake hira da manema labarai ranar Litinin, gwamna Abiodun ya tabbatar da batun zantawarsa da gwamnan CBN bayan takardarsa ta isa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Amfani da Tsoffin Kudi N500 da N1000 Bayan Umarnin Kotu

Ya ce Emefiele ya amince da umarnin Kotun koli, wanda ya tsawaita wa'adin amfani da tsohon kuɗi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar gwamnan, bisa la'akari da matsin da sabon tsarin ya jefa mutane da kuma tausayin al'umma, ya zama wajibi mahukunta su yi wani abu da zai yaye wa mutane halin da suka tsinci kansu.

A kalamansa ya ce:

"Da kaina na yi magana da gwamnan babban banki CBN, Mista Godwin Emefiele, kuma ya yi alkawarin zasu tsawaita wa'adin da CBN ya gindaya a baya game da tsohon kuɗi domin biyayya ga Kotu."
"Ina farin cikin sanar da ku cewa waraka na nan tafe ga 'yan Najeriya game tsarin sauya fasalin naira. Dukkan mu zamu yi murna cikin jin daɗi daga karshe."

Idan baku manta ba, gwamna Abiodun ya gargaɗi bankunan kasuwanci da su guje wa sabawa hukuncin Kotun koli kan tsoffin takardun kuɗi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsofaffin Kudi: Gwamnoni Sun Kuma Yin Taron Dangi, Sun Ba Gwamnatin Buhari Wa’adi

Ku daina baiwa Mutane Tsoffin Naira Idan Ba Zaku Karba Ba, Adeleke Ga Bankuna

A wani labarin kuma Gwamnan PDP Ya Harzuka, Ya Umarci Bankuna Su Daina Baiwa Mutane Tsohon Kuɗi

Gwamnan Osun ya ce ya samu labarin zaluncin da wasu bankuna su ke yi na baiwa mutane tsoffin kuɗi amma idan aka kawo musu ajiya ba su karba.

Ademola Adeleke ya ce ba zai yarda bankuna na aikata haka ba a jiharsa, ya bukaci CBN ya ɗauki mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel