Ku daina baiwa Mutane Tsoffin Naira Idan Ba Zaku Karba Ba, Adeleke Ga Bankuna

Ku daina baiwa Mutane Tsoffin Naira Idan Ba Zaku Karba Ba, Adeleke Ga Bankuna

  • Gwamnan Osun ya gargaɗi bankunan kasuwanci su dakatar da baiwa mutane tsohon kuɗi idan ba zasu karɓa ba
  • Adeleke ya yi kira ga CBN ya gaggauta kawo karshen wannan ɗabi'a mara kyau da bankuna suka bullo da ita
  • Ya ce ya samu korafe-korafe cewa bankuna na ƙin karban ajiyan tsohon kuɗi duk da suna baiwa mutane

Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya gargaɗi bankunan da ke da rassa a jihar su dakatar da baiwa mutane tsohon naira idan har ba zasu karɓa ba idan an kawo musu ajiya.

Daily Trust ta tattaro cewa Adeleke ya yi wannan gargaɗi ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Olawale Rasheed, ya fitar ranar Litinin a Osogbo.

Gwamna Adeleke na Osun
Ku daina baiwa Mutane Tsoffin Naira Idan Ba Zaku Karba Ba, Adeleke Ga Bankuna Hoto: dailytrust
Asali: Depositphotos

Gwamnan ya ce zaluncin da bankuna su ke wa kwastomominsu ta hanyar biyansu da tsohon kuɗi amma su ki karba idan sun dawo musu, babban abin damuwa ne.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai Ya Fusata, Ya Shirya Tona Asirin Tsaffin Ɓarayin Gwamnonin Jihar Kaduna

Ya ce ya karbi korafe-korafe da dama daga mazauna masu mu'amala da bankuna, waɗanda suka zargi bankuna da ƙin karban tsohon naira daga hannunsu da kuma wulaƙanci kala-kala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeleke ya ce:

"Na samu kira daga kwastomomin bankuna na faɗin jihar nan, rashin karban takardun tsohon naira da bankuna suka ɗauri ɗamarar yi ya ƙara haifar da matsala ga rayuwar mutane."
"Ba zai yuwu bankunan da suka baiwa mutane tsohon takardun naira kuma a ce ba su karba idan an zo a ajiya, ba zamu lamurci haka ba."

Bugu da ƙari, gwamna Adeleke ya yi kira ga CBN ya dawo hayyacinsa ya umarci bankuna su gaggauta gyara wannan kurkuren da suke aikatawa.

A rahoton Vanguard, gwamnan ya ci gaba da cewa:

"Muna kira ga Daraktan CBN na jiha ya umarci bankuna su dakatar da wannan gurbatacciyar ɗabi'ar. Idan bankuna ba zasu karbi tsoffin kuɗin ba to su daina biyan mutane da su."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan CBN Ya Umurci Bankuna Su Fara Fitar da Tsaffin Kudi, Gov Soludo

Karya ake mun - Gwamnan CBN ya musanta zargin kulla wa Tinubu sabon tuggu

A wani labarin kuma Gwamnan CBN Ya Musanta Rahoton Cewa Yan Kulla Wa Tinubu Sabuwar Makarkashiya

Gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele, ya karyata labarin da ake yaɗawa cewa ya shiryawa Tinubu sabon tuggu a zaben gwamna mai zuwa. Mista Emefiele ya ce shi ba ɗan siyasa bane kuma ba ya tsoma baki, ya roki 'yan Najeriya su yu watsi da labarin na ƙarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel