Shugaban APC Na Kasa Ya Amince An Samu Aibi a Zaben da Tinubu Ya Yi Nasara

Shugaban APC Na Kasa Ya Amince An Samu Aibi a Zaben da Tinubu Ya Yi Nasara

  • Shugaban APC na kasa ya amince cewa an samu naƙasu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023
  • Abdullahi Adamu ya ce a tarihin duniya babu inda aka gudanar zabe cikakke babu lahani ko kwara ɗaya
  • A cewarsa, shugaba Buhari ya yi alkwarin gudanar da sahihin zaɓe kuma ya cika maganarsa

Abuja - Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 ba cikakken mara naƙasu bane.

Adamu ya faɗi haka ne sa'ilin da yake jawabi a wurin taron kwamitin gudanarwa na APC da shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima da zababbun mambobin majalisar tarayya.

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu.
Shugaban APC Na Kasa Ya Amince An Samu Aibi a Zaben da Tinubu Ya Yi Nasara Hoto: APC Nigeria
Asali: Facebook

Taron wanda suka yi a sirrince ya gudana ne a State House Banquet Hall da ke babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin Mukaman Da Gbajabiamila, El-rufai, Kudu Maso Gabas Ka Iya Samu a Gwamnatin Tinubu

Daga cikkin manyan jiga-jigan da suka halarci taron har da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gabajabiamila, ministan ayyuka, Babatunde Fashola, da sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan taron na zuwa ne yayin da mambobin NWC suka fara kiran a sake fasalin jagorancin jam'iyyar kuma Adamu ya yi murabus domin saita tikitin Musulmi da Musulmi na gwamnati mai zuwa.

An samu ɗan aibu a zaben da ya gabata - Adamu

Da yake jawabi a wurin taron, Adamu ya taya kafatanin zababbun yan siyasan murna inda ya ce sun cancanci haka bayan samun nasara a zaben 25 ga watan Fabrairu.

Shugaban APC, wanda ke fama da fafutukar kare kujerarsa, ya amince cewa zaɓen da ya gabata wansa ya ayyana su a matsayin masu nasara yana da naƙasu.

Ripple ta rahoto a jawabinsa yana cewa:

Kara karanta wannan

Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja

"Ina taya ku murna daga ƙasan zuciyata, na jinjina muku kuma ku ne sabon zubin Najeriya. Daga ranar 29 ga watan Mayu, duk wani zancen haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba zai dawo wuyanku."
"Adalci ne mu amince cewa zaben 25 ga watan Fabrauru ba cikakke bane, dama bamu shirya gudanar da cikakken zaɓe ba, a tarihin duniya babu inda zabe ya gudana cikakke babu naƙasu."
"Kamar sauran ƙasashen Demokuraɗiyya, mun shirya gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe, wannan kam mun cika. Ina alfahari mun cimma nasarar cika alƙawarin da shugaba Buhari ya yi wa mutane."

NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Naira da Fetur

A wani labarin kuma ƙungiyar kwadugo ta ƙasa NLC ta baiwa gwamnatin shugaba Buhari wa'adin mako ɗaya ta gaggauta kawo ƙarshen karancin naira da Fetur.

Shugaban kungiyar na kasa ya bayyana tsauraran matakan da zasu ɗauka a faɗin Najeeiya idan wa'adin ya cika gwamnati ba ta magance matsalolin ba.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: An Fallasa Ɗan Takarar Shugaban Kasan da Peter Obi Ya Yi Wa Aiki a Zaɓen 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel