Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Sace Uba Da ’Ya’yansa 4 a Zamfara

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Sace Uba Da ’Ya’yansa 4 a Zamfara

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka sace mutum biyar nan take a wani yankin a jihar Zamfara
  • A cewar majiyar dangi, an sace uba ne da ‘ya’yansa hudu, lamarin da ya tada hankalin matar gida da ‘yan sojoji
  • Ana yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankuna daban-daban na jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya

Jihar Zamfara - An sace wani mahaifi, Mr Moruf tare da ‘ya’yansa hudu a gidansa da ke Saminaka a karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Matar mutumin, Mrs. Aisha da danta ne ba a sace ba a cikin a harin, kamar yadda rahoton gidan talabijin na TVC News ya bayyana.

‘Yan bindigan, a cewar matar sun mamaye gidan ne dauke da muggan makamai da misalin karfe 2 na daren ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnoni: Yadda 'yan siyasa ke tada hankalin mazauna jihar Arewa da muggan 'yan daba

Yadda 'yan bindiga suka sace mutum da 'ya'yansa hudu a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara mai fama da 'yan bindiga | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An ceto yara biyu daga cikin hudu

Sa’o’i kadan daga baya, jami’an rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar ceto biyu daga cikin yaran da aka sace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ceto su ne a cikin wani daji yayin da mahaifin da kuma sauran yaran biyu kuma ‘yan bindigan suka tsere tare dasu.

A cewar matar:

“Sun kutsa kansu zuwa cikin gidanmu ne kusan karfe 2:00 na dare a yau kuma suka sace mijina da hudu daga cikin ‘ya’yanmu.
“Na sanar da ‘yan sanda da wasu sojoji game da abin da ya faru kuma nan da nan suka fara daukar mataki.
“Sa’o’i kadan bayan faruwar lamarin, da misalin karfe 12 na rana sojoji suka kira suka sanar damu sun samo ‘ya’yana biyu, amma mijina da sauran ‘ya’ya biyun ‘yan bindiga sun tafi dasu.”

Yadda ‘yan bindiga ke ta’addanci a Zamfara

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga, sun ceto wani fitaccen dan jarida

Wannan lamarin dai shine ya faru a baya-bayan nan bayan da sojojin Operation Hadarin Daji suka dakile harin ‘yan bindiga a karamar hukumar Kaura Namoda na jihar.

An sace mutum 14, ciki har da yara kanana da mata masu shawarwa, inda ‘yan sanda suka yi nasarar ceto su.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da ke yawan ganin hare-haren ‘yan bindiga a irin wannan lokacin.

A baya kun ji yadda fada tsakanin 'yan banga da 'yan bindigan ya kai ga mutuwar mutum 18 a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel