'Yan Sanda Sun Yi Ruwan Wuta, Sun Ceto Dan Jaridan da Aka Sace a Ranar Alhamis

'Yan Sanda Sun Yi Ruwan Wuta, Sun Ceto Dan Jaridan da Aka Sace a Ranar Alhamis

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi nasarar fatattakar wasu 'yan bindigan da suka sace wani dan jarida
  • Rahoto ya bayyana yadda tsagerun suka sace dan jarida tare da neman kudin fansan da ya kai N30m
  • Ya zuwa yanzu, an fatattaki 'yan bindigan, inda wasu da yawa suka gudu da raunukan harbin bindiga

Jihar Legas - Jami’an ‘yan sanda sun ceto wani dan jarida, Seun Oduneye daga hannun ‘yan bindiga bayan musayar wuta da suka yi da ya kai mintuna 45.

Oduneye, wanda shine mai gidan jaridar Issues Magazine ya shiga hannun tsagerun ne a yankin Mobalufon a Ijebu Ode a ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito.

Dan jaridan na kan hanyarsa ta zuwa Ijebu Ode ne daga Abeokuta lokacin da ya gamu da ‘yan bindiga a yankin na Mobalufon.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane 5 Da Ke Hako Gawarwaki A Makabarta Suna Sayar Da Sassan Jikinsu A Ogun

'Yan sanda sun ceto dan jarida
Tambarin rundunar 'yan sandan Najeriya | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

An ruwaito cewa, a lokacin da lamarin ya faru, yana tuka motarsa ce kirar Toyota Camry da misalin karfe 7:50 na yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Washe-gari, ‘yan bindigan sun kira matarsa tare da sanar da ita cewa yana hannunsu, kuma sai an ba da kudin fansa N30m kafin su sako shi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Abimbola Ayeyemi ya fada a ranar Litinin cewa, an yi nasarar ceto dan jaridar daga maboyar ‘yan bindigan.

Matakin da 'yan sanda suka dauka tun farko

A cewarsa, bayan samun rahoton sace dan jaridan, kwamishinan ‘yan sandan, Frank Mba ya umarci babban jami’in ofishin yanki na ‘yan sanda a Obalende, SP Murphy Salami da ya tabbatar da ceto dan jaridan, The Guardian ta ruwaito.

Oyeyemi ya ce, jami’an sun yi aiki da sashen bincike da ‘yan sanda daga jami’an Idimu a jihar Legas don gano inda ‘yan bindigan suke.

Kara karanta wannan

Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja

Bayan musayar wuta, ‘yan bindigan sun yi watsi da dan jaridar, inda suka tsere da raunukan harbin bindiga.

'Yan bindiga da 'yan banga sun yi musayar wuta a Katsina

A Arewacin Najeriya kuwa, kunji yadda musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da 'yan banga ya kai ga mutuwar mutane da yawa.

Wannan lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar hare-hare daga 'yan bindiga masu kisa.

A cewar majiya, akalla mutum 18 ne suka mutu a lokacin da tsageerun 'yan bindigan suka farmaki jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel