Mazauna Sokoto Na Zaman Dar-Dar Ganin Yadda ’Yan Siyasa Ke Kamfen Mai Tada Hankali

Mazauna Sokoto Na Zaman Dar-Dar Ganin Yadda ’Yan Siyasa Ke Kamfen Mai Tada Hankali

  • Jam’iyyun siyasa a jihar Sokoto na ci gaba da ganin laifin juna yayin da rikici ke kara barkewa a tsakaninsu a kwanakin nan
  • Mazauna a jihar na ci gaba da zaman dar-dar yayin da ake fuskantar zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a fadin kasar
  • Hukumomin tsaro da Mai Girma Sarkin Musulmi sun yi kira ga zaman lafiya, ‘yan sanda sun kaddamar tawagar yaki da ‘yan daban siyasa

Jihar Sokoto - Ana zaman dar-dar a jihar Sokoto yayin da zaben gwamna ke kara gabatowa a jihar, inda kalaman wasu ‘yan siyasa ke tada hankalin jama’a.

Yanayin siyasar jihar ya dauki dumi tun bayan da kalamai, cece-kuce da zarge-zarge suka fara yawa bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Idan baku manta ba, an samu tashe-tashen hankula a zaben, inda aka soke sakamakon zaben rumfunan zabe sama da 400, inda hukumar zabe ta INEC ta gaza sanar wadanda suka lashe zabe a jihar har zuwa yau.

Kara karanta wannan

Bwacha: Kwanaki Kadan Suka Rage a Zabi Gwamna, APC Ta Dakatar da ‘Dan Takaranta

Yadda 'yan siyasa ke tada hankalin jama'a a Sokoto
Jihar Sokoto a Arewacin Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yadda ‘yan siyasa ke tada hankalin jama’a

An tattaro cewa, ‘yan takara da jam’iyyunsu a jihar sun yi amfani da ‘yan daba wajen barnata rumfunan zabe a jihar, wanda hakan ne ya kai ga soke sakamakon zaben.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai rahotannin da ke bayyana cewa, wasu ‘yan daba sun fatattaki masu kada kuri’u tare da lalata akwatunan zabe da kuri’u a wasu yankunan.

A yankin Bazza na karamar hukumar Sokoto ta Arewa, an ruwaito cewa, ‘yan daba sun fatattaki masu kada kuri’u tare da lalata kayan aikin zaben.

Wani mazaunin yankin, Muhammad Bazza ya shaidawa majiyar Daily Trsut cewa, ‘yan siyasan da suka hango faduwa a zaben ne suka dauki nauyin aikin ta’addanci a rumfunan zaben.

A bangaren karamar hukumar Shuni, wani Isa Abubakar ya bayyana yadda ‘yan a mutun wata jam’iyya suka dagula zaman lafiyar rumfunan zabe da yawa a yankin.

Kara karanta wannan

Da walakin: Tinubu zai gana da zababbun 'yan majalisu da sanatoci kan wata bukata daya

PDP na ganin laifin APC, APC na ganin laifin PDP

A halin da ake ciki, jam’iyyun siyasa na APC da PDP na ci gaba da ganin laifin juna wajen tashin rikicin siyasa a jihar ta Sokoto.

Hakazalika, dukkan jam’iyyun biyu sun yi Allah-wadai da abin da ya faru, inda suka yi kira ga INEC da ta dauki matakin da ya dace.

A bangare guda, jam’iyyar APC ta nemi jami’an tsaro da su dauki mataki, inda tace jam’iyyar PDP mai ci a jihar ce ke kawo duk wani tsaiko.

A tun farko, sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su kasance masu mutunta juna.

Martanin ‘yan sanda

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Useini Gumel ya ba da umarnin kama duk wani dan daban siyasa da masu daukar nauyin ta’addanci a jihar.

Ya bayyana wannan umarnin a yayin kaddamar da tawagar Operation ‘Kule Chas’ da ke da manufar yakar ‘yan daban siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Fada ta barke tsakanin 'yan bindiga da 'yan banga a jihar su Buhari, an kashe mutane da yawa

Hakazalika, kwamishinan ya ce, jami’ansa su kame duk wani wanda yazo belin a saki dan daban da aka kama a irin wannan yanayin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel