Bwacha: Kwanaki Kadan Suka Rage a Zabi Gwamna, APC Ta Dakatar da ‘Dan Takaranta

Bwacha: Kwanaki Kadan Suka Rage a Zabi Gwamna, APC Ta Dakatar da ‘Dan Takaranta

  • Shugabannin Jam’iyyar All Progressives Congress na Donga, za su ladabtar da Emmanuel Bwacha
  • Ana zargin ‘dan takaran Gwamnan da laifuffuka da-dama, sai aka dakatar da shi daga Jam’iyya
  • Sanata Bwacha ya karyata labarin, ya ce abokan adawarsa a zaben tsaida gwani ne suke yakar shi

Taraba - A maimakon rikicin cikin gidan APC ya lafa, mun fahimci ya kara jagwagwalewa bayan dakatar da Emmanuel Bwacha mai takarar Gwamna.

A rahoton Punch na safiyar Litinin, mun ji jam’iyyar APC ta dakatar da Emmanuel Bwacha bisa zargin yana hada-kai da ‘yan adawa, yana shirya zagon kasa.

Shugabannin APC sun bukaci Sanata Emmanuel Bwacha ya tsaida duk wani kamfe da yake yi, da sunan cewa hakan ya saba doka, ya bayyana a gaban kwamiti.

Ana so a yau Litinin, Sanatan ya je gaban kwamiti na musamman da aka kafa domin ya yi bincike a kan shi, da nufin gano gaskiyar zargin da su ke kan wuyansa.

Kara karanta wannan

Da Sauran Rigima, Gwamna Wike Ya Jero Wadanda Za a Fatattaka Daga Jam’iyyar PDP

Kwamiti zai yi bincike

An kafa kwamitin ne bayan an kai korafi a kan ‘dan takaran, hakan ya dawo da shi baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar ta ce ta tuntubi Sanata Bwacha domin jin ta bakinsa, sai ya nuna labarin ba gaskiya ba ne, ya ce aikin ‘yan adawa ne da ya doke wajen samun takara.

Kamfe
Kamfen APC a zaben 2023 Hoto: @thenationng
Asali: Facebook

Bwacha yake cewa idan aka duba sa hannun, za a fahimci babu ruwan shugabannin mazabun jam’iyyar APC na reshen Mararaba a karamar hukumar Donga.

Wasikar dakatar da Emmanuel Bwacha

Abin da wasikar ta ce shi ne an kawo karar ‘dan takaran kan zargin rashin da’a, zagon-kasa, yin ba daidai ba game da hukuncin kotun tarayya na FHC/CS/13/2022.

Har ila yau, an tuhumi ‘dan majalisar na Kudancin Taraba da kin yin biyayya ga hukuncin kotun koli a shari’ar David Sabo Kente da Sanata Emmanuel Bwacha.

Kara karanta wannan

Nwosu: Za a Fara Zaman Makoki a APC, Shugaba a Jam’iyya Ya Rasu a Asibiti

Zargi na uku shi ne jawowa jam’iyyar bakin jini da cin mutunci, wanda hakan ya saba dokar APC.

A karshe aka datar da Emmanuel Bwacha, aka bukaci ya kare kan shi a kwamiti. Wasikar ta ce an sanar da INEC da jami’an tsaro game da wannan mataki.

Makarkashiyar CBN a Legas

Bayan APC ta lashe zaben Shugaban kasa, an samu labari cewa Gwamnan CBN yana taimakawa Jam’iyyar LP a Legas a zaben Gwamnoni da za a shirya.

Godwin Emefiele ya yi amfani da bankin CBN, ya ba ‘Dan takaran LP Naira miliyan 500 domin yin kamfe a lokacin da ake fama da karancin takardun kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel