APC Ta Hada Zama Tsakanin Tinubu da Zababbun ’Yan Majalisun Tarayya a Najeriya

APC Ta Hada Zama Tsakanin Tinubu da Zababbun ’Yan Majalisun Tarayya a Najeriya

  • Jam’iyyar APC ta bayyana bukatar ganawa da dukkan zababbun ‘yan majalisu da sauran masu ruwa da tsaki a kasar nan
  • APC na son samawa zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu wadanda za su taimaka masa wajen tafiyar da mulki
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana kan ingancin lashe zaben shugaban kasa na Bola Ahmad Tinubu da APC

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta tsara wani taron ganawa da Bola Ahmad Tinubu, Kashim Shettima da sauran zababbun sanatoci da ‘yan majalisun taraya.

A cewar rahoto, za a yi wannan ganawar ne a ranar Litinin 13 ga watan Maris, 2023 a babban birnin tarayya Abuja, BBC ta ruwaito.

Tattaunawar APC da zababbun shugabannin za ta mai da hankali ne ga kawo hanyoyin zabar shugabannin majalisun kasar guda biyu.

Kara karanta wannan

Barau Jibrin Ya Shiga Takarar Kujerar Shugaban Majalisa, Ya Gana Da Zababbun Sanatoci 70

Tinubu zai gana da 'yan majalisun tarayya
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Za a samar da shugabanni daban-daban na shiyyoyi

Hakazalika, zaman zai yi duba ga yadda za a raba mukamai daban-daban daga majalisun ga shiyyoyi daban-daban na kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Iyiola Omisore, sakataren jam’iyyar APC na kasa ne ya bayyana hakan a kafar Twitter, inda yace ganawar za ta fara ne a ranar Litinin da misalin karfe 12:00 na rana.

Bayan kammala zaben shugaban kasa a Najeriya, INEC ta sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe, yanzu dole a samar da wadanda za su ba shi sauki wajen gudanar da mullki

Abubuwan da ake bukata kowane zababben dan takara

A bangare guda, jam’iyyar ta APC ta bukaci dukkan zababbun shugabannin da su hallara a taron da takardun shaidan lashe zabe da hukumar INEC ta ba su.

Idan baku manta ba, ‘yan majalisu da dama a Najeriya snan sun fara bayyana sha’awarsu ta zama shuganannin majalisun dokokin kasar nan guda biyu.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisa Ya Ki Karbar Satifiket Din INEC, Yana Harin Mukami Kusa da Tinubu

Bola Ahmad Tinubu zai samu saukin tafiyar da mulkinsa ne idan aka samu hadin kai tsakanin shugabannin majalisun kasar biyu; na dattawa da majalisar wakilai.

Yarbawa sun ce basu yarda Tinubu ne ya ci zabe ba

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta bayyana nesanta kanta da nasarar Bola Ahmad Tinubu ya samu a zaben 2023 da aka yi.

Kungiyar ta ce, Peter Obo na jam’iyyar Labour ne ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu.

Hakazalika, ta zargi hukumar zabe ta INEC da kitsa komai kan yadda aka ambaci Tinubu ne ya samu nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel