Karancin Kudi: Gwamnatin Kogi Za Ta Kama, Hukunta Mutane, Kamfanoni Da Ke Kin Karbar Tsaffin Naira

Karancin Kudi: Gwamnatin Kogi Za Ta Kama, Hukunta Mutane, Kamfanoni Da Ke Kin Karbar Tsaffin Naira

  • Gwamnatin jihar Kogi tana barazanar kama tare da hukunta duk wani mutum da kamfani ko kasuwanci da ke kin karbar tsaffin kudi a jihar
  • Gwamnatin ta yi imanin cewa rashin karbar tsaffin kudin saba umurnin kotun koli ne
  • Babban bankin na kasa, CBN, ta yi shiru kan hukuncin da kotun kolin ta yi na tsawaita wa'adin cigaba da amfani da tsaffin kudin zuwa Disamban 2023

Jihar Kogi - Gwamnatin Jihar Kogi ta gargadi daidaikun mutane da kamfanoni wadanda ke kin karbar tsaffin takardun naira a jihar cewa za a iya kama su tare da hukunta su, Daily Trust ta rahoto.

A cewar kwamishinan labarai da sadarwa, Kingsley Fanwo, wannan matakin saba umurnin kotun koli ne karara inda ta ce a cigaba da amfani da sabbi da tsaffin kudin har zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Da Zafi-Zafi: Jam'iyyar Labour Ta Yi Barazanar Mamaye Ofisoshin INEC Na Kasa Baki Daya, Ta Bayyana Dalili

Kudin Najeriya
Wasu yan Najeriya na cigaba da kin karbar tsaffin kudi. Hoto: CBN
Asali: Getty Images

Fanwo, cikin sanarwar da ya fitar, ya yi kira ga mutanen jihar su kai rahoton marasa karbar tsaffin kudin, ya kuma ce za a rufe duk wani banki da ke kin karbar tsaffin kudin.

Ya ce ba za a amince ba wasu mutane da kamfanoni su cigaba da kin karbar tsaffin kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya yi kira ga mazauna Kogi su kai karar duk wani wanda bai karbar tsaffin kudin ga hukumomin da suka dace.

Tribune ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kogin ta ce za ta rufe duk wani banki da bai karbar tsaffin kudin domin gwamnatin jihar ba za ta amince da duk wani banki da ke saba umurnin banki mafi girma a kasa.

Sanarwar ta kuma ce gwamnatin na Kogi ta kafa kwamiti da zai tabbatar an bi umurnin kotun kolin.

Yan Najeriya sun yi martani

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamna ya roki 'yan jiharsa, ya fadi abin da ya kamata su yi idan aka basu tsoffin Naira

Suleiman Yusuf, a shafinsa na Twitter ya rubuta:

"Idan yan kasuwa sun karbi kudin, ta yaya za su saka a banki"

Abraham Christiana ya ce:

"Tsohon kudi, sabbin kudi babu tsabar kudi a kasar"

Amoketun sun kama wani mutum dauke da tsabbar sabbin kudi N250,000 na bogi

A wani labarin mai kama da wannan, jami'an hukumar tsaro na kudu maso yamma wato Amotekun sun kama wani mutum, Celestine da takardun naira na bogi da adadin su ya kai N250,000.

Hakan na zuwa ne a lokacin da mutanen Najeriya ke fama da karancin kudaden a sassa daban-daban

Wanda aka kama din, Celestine, ya yi ikirarin cewa shi dan kasuwa ne kuma haifafan Anambra amma yana zaune a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel